Akasari Hausawa a Nijeriya, na kiran wannan bera da beran masar, wanda wata sabuwar hanyar kiwonsa ta bulla a wannan kasar.
Haka zalika, fannin kiwon nasa na sake zama wata sananniyar hanya a fadin wannan kasa, musamman ganin cewa ana samun kudaden shiga daga fannin.
- Zaben Fitar Da Gwani Na APC A Edo Ya Bar Baya Da Kura
- Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar
Beran masar wani dangi ne daga zomo, inda fara kiwonsa bai da wata wahala; sannan abincinsu ya kasance daga kayan ganyayyaki, kazalika suna iya jure wa kowane irin yanayi da suka samu kansu, ana kuma iya kiwon su a ko’ina.
Matakan Fara Kiwonsa A Nijeriya:
1- Sayen Beran Masar:
Ka tabbatar beran masar din da za ka sayo, domin kiwo lafiyayye ne, musamman don ya haifa maka lafiyayyun ‘ya’ya tare da samun riba idan ka tashi sayarwa.
Har ila, ana samun nau’ikan wannan bera iri daaban-daban idan tashi saya don kiwatawa ko kasuwanci.
2- Bashi Kulawar Da Ta Dace:
Idan har kana so ka samu nasara a fannin kiwon beran masar, dole ne ka tabbtar kana ba su kulawar da ta dace, kamar ciyar da su lafiyayyen abinci, tsaftatattacen ruwan sha, samar musu da dumi, musamman a lokacin sanyi; ya zama wajibi ka rika ba su kariya daga sauran dabbobin da za su iya cutar da su ko kashe su.
4- Sama Musu Dakin Kwana:
Wannan ne matakin farko da ya kamata mai son ya yi kiwon beran masar ya kiyaye kafin ya sayo su, don fara kiwon su.
Haka zalika, akwai nau’ika biyu na samar musu da dakin kwana; wanda ake sanya su a cikin keji, sai kuma wanda ake zuba su a fili wadatacce yadda za su rika watayawa yadda suke so, inda ake son filin ya kasance zai iya daukar yawan beran kamar guda 20 zuwa 30.
5- Ciyarwa:
Ana bukatar wanda zai yi kiwon su ya tabbatar yana ba su wadataccen lafiyayyen abinci, musamman domin su girma da wuri tare da samar da wadataccen nama.
Abincinsu ba shi da wani wuyar samu, domin kuwa sun fi cin kayan lambu.
6- Sanya Masu Maniyyin Wata Dabbar:
A wannan matakin, wanda ke kiwon beran masar zai iya yi samo maniyin wata dabbar daban, domin sanya wa macen beran masar, don samun wani irin dan na daban.
7- Sayawa:
Ka tabbata ka kai su kasuwa mafi kusa tare da samo wadanda za su saya da yawa a lokaci guda, domin samun gwaggwabar riba.
Alfanunsa Na Da Dama, Amma Ukun Da Aka Fi Sani Su Ne:
1- Karuwar Bukatarsa:
Ana matukar bukatarsa da yawa, sakamakon yadda namansa yake da dadi, musamman ganin yadda yara ke son kiwon sa.
2- Samar Da Wadataccen Nama:
Koda-yake, ba kowa ne ya ke iya cin namasa ba, amma ta hanyar kiwonsa za a iya samar da wadataccen namansa, sannan kuma yana dauke da sinadaran ‘protein da cholesterol’.
3- Bincike A Fannin Fasaha:
Ana yin amfani da shi don yin gwaje-gwaje a fannin fasaha kamar a asibitoci da dakunan gudanar da bincike na fannin kiwon lafiya na amfani da shi wajen samar da magunguna.