Hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Nijeriya da ma Afirka gaba daya. Ta nan ne ake samar wa masana’antunmu na ciki da wajen kasa kayan sarrafawa, wanda kuma hakan ke samar da aikin yi ga dimbin matasa a ciki da wajen kasar nan.
A Nijeriya, tarihi ya nuna irin tasirin ma’adanai ga tattalin arzikin kasa inda ake samun fiye da kashi 0.3 na arzikin kasa daga bangaren ma’adanai (kamar yadda bayani ya nuna a kasafin kudin shekarar 2022). Bincike ya kuma nuna cewa, a yankin Afirka ake samun kashi 30 na dukkan ma’adanai na duniya, lamarin da ya sa Afirka a sahun gaba a harkar ma’adanai na duniya.
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
- Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamna A Legas Za Ta Yanke Hukunci Ranar Litinin
Duk da kasancewar harkar hakar ma’adanai na da muhimmanci ga tattalin arzikin Nijeriya amma har zuwa yanzu ba a kai ga bunkasa sashin ba yadda ya kamata, saboda rashin cikakken kayan aiki na zama da rashin masu zuba jari da kuma yadda har yanzu ake ci gaba da amfani kayan aikin hakar ma’adanai ba na zamani, uwa uba kuma yadda masu hakar ma’adanai ba tare da izini ba suka mamaye bangaren. Wannan kuma yana samun bunkasa ne saboda yadda aka yi sakaci har ‘yan kasashe waje suka shigo suka mamaye bangaren suma suna hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba. Masana sun bayyana yadda hakar ma’adanai ba tare da cikakken izini ba ke cutar da muhalli da al’umma gaba daya.
A ‘yan shekarun nan gwamnati ta dauki matakai na ganin an farfado da bangaren hakar ma’adanai, musamman ganin ana ganin lokaci ya yi da za a duba wasu bangarori don nema wa Nijeriya kudaden shiga saboda ganin yadda kasuwar albarkatun man fetur yake komawa baya.
Gwamnati ta dauki matakai masu muhimmanci don jawo hankalin ‘yan kasuwa da masu zuba jari na ciki da wajen kasa don su shigo a dama da su a harkar hakar ma’adanai a Nijeriya, kuma daga dukkan alamu wannan matakai sun fara haifar da da mai ido.
Ga wanda yake son fadawa harkar hakar ma’adanai a Nijeriya ga wasu matakai masu muhimmanci da za su iya taimaka masa don gudanar da harkar kamar yadda doka ta tanada.
1). Samun Lasisi Daga Hukuma: kafin fara hakar ma’adanai yana da kyau mutum ya nemi izinin gwamnati ta hanyar samun lasisi na irin harka ma’adanan da zai yi. Laisisin da ake bayarwa sun hada da na masu dan karamin karfi da kuma na manya-manyan kamfanoni. Lasisin kuma zai iya kasancewa na mai haka kai staye ko mai sarrafawa, ko kuma na masu tsotso ruwa suna sayarwa, wato kamar masu ‘Fiya wata’ duk sai sun samu lasisi, ana kuma samun lasisin ne a karkashin ofishin gwmanati mai suna ‘Nigerian Cadastre’ wanda sune ke da alhakin sa ido a kan dukkan harkokin hakar ma’adanai a Nijeriya. A kwai kuma bukatar mutum ya nemi cikakken bayani na yadda ofishinsu ke aiki don ya samu saukin yin rajistar. Haka kuma cikin sharuddan dole mutum ya yi rajistar kamfaninsa tare da hukumar yi wa kamfanoni rajista a Nijeriya wato “Cooperate Affairs Commission” don sunan kamfanin mutum ya shiga cikin jerin kamfanoni da ke harkokinsu a Nijeriya, wannan na da matukar muhimmanci.
2). Bayanin Yadda Za A Gudanar Da Kasuwancin Ma’adanan ‘Business Plan’:
Akwai bukatar a samu cikakken bayani na irin ma’adanan da ake son fara haka da inda ake samunsu, yana kuma da muhimmanci a gudanar da bincike na kimiyya don sanin yawan ma’adanan a yankin, saboda ganin irin jarin da za a zuba.
3). Binciken Wurin Da Ake Son Gudanar Da Hakar Ma’adanan
Wannan kuma bincike ne na musamman da kwararru ke gudanarwa a wurin da ake son fara hakar ma’adanan don a gano hakikanin yawan ma’adanan da ke a cikin kasa, ta haka za a iya fahimtar yawa da ingancin ma’adanan don kada masu zuba jari su yi asara.
4). Binciken Kimiyya:
Binciken kimiyya a wurin da ake sa ran hakar ma’adanai yana bayar da bayanai don gane ainihin yawan ma’adanain da ake da shi a kasa da kuma yawan da za a iya hakowa a kullum. Wannan yana bayar da daman tsara yadda za a fuskanci aikin da yawan ma’akatan da ake bukata don samun cikakkiyar nasara.
5). Samar Da Kayyakin Aiki Na Zamani:
Yana da matukar muhimmanci samar da kayan aiki na zamani da za a gudanar da aiki a cikin sauki, wannan kuma ya hada da motoci na daukar ma’adanai da aka hako da muka ma’aikata.
6). Samar Da Wutar Lantarki Da Gidajen Ma’aikata
Yana da muhimmanci a samar da wurin kwana ga ma’aikata, yana kuma da kyau a gina gidan nesa da wurin da ake hakar ma’adanan saboda kariya daga cutar da ma’aikatan daga turirin ma’adanan da ake hakowa. Haka kuma samar da wutar lantarki na NEPA ko janaretab zai taimaka.
7). Fara Hakar Ma’adanan Gadan-gadan:
Daga nan kuma sai a fara aiki don ci gajiyar ma’adanan da aka shirya haka, ana taftacesu tare da wucewa da su kasuwa a ciki ko wajen kasa.
Yana kuma da muhimmanci a shigar da Sarakuna gargajiya da shugabanin matasa na yankin da ake hakar ma’adanan don kasancewa cikin jerin ma’aikata ko ‘yan kwangon da za su samar da wasu kayyakin aiki a ma’aikatar, wannan yana da matukar muhimmanci don rage kishi na ganin ana kwashe masu albarkatun kasa su kuma basu ci gajiyar abin ba. In har aka shigar da su, su da kansu za su ba harkar kariya daga duk wani abin da zai cutar da tafiyar saboda suma suna amfana. A na gaba za mu kawo muku irin ma’adanan da Allah ya shimfida a sassan Nijeriya.