Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Legas na shirin yanke hukunci kan karar da ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party (LP), Gbadebo Rhodes-Vivour suka shigar.
Sauran wadanda suka shigar da karar a kwai jam’iyyar PDP da dan takararta, Olajide Adediran, (Jandor). Za a yanke hukuncin ranar Litinin, 25, ga Satumba 2023.
- INEC Ta Dage Zabe A Wasu Rumfuna 10 A Jihar Legas
- Zaben Gwamnoni: ‘Yan Sanda Za Su Hukunta Masu Yada Labaran Karya A Legas
Mai shari’a Arum Ashom ne zai jagoranci zaman kotun kamar yadda aka da dukkan bangarorin a ranar Asabar.
Rhodes-Vivour da Jandor suna kalubalantar nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Mataimakin Gwamna Obafemi Hamzat na Jam’iyyar APC tare da ayyana su a matsayin wadanda suka lashe zaben Gwamnan Jihar Legas da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi a ranar 18 ga Maris.