Matakan Sin Na Samun Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Za Su Taimaka Wajen Farfado Da Lafiyar Duniya

Daga CRI Hausa

Yau ranar 22 ga watan Afrilu, ranar duniya ce karo na 52. Taken ranar a wannan karo shi ne gyara muhallin duniyarmu.
Gabanin zuwan wannan rana, jami’in mai kula da harkokin nahiyar Afirka na hukumar shirin kiyaye muhalli, da aikin kula da albarkatun halittu ta MDD Lewis Kahwaji, ya bayyanawa ‘yan jarida na kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya a birnin Nairobin kasar Kenya cewa, Sin ta kiyaye daukar matakan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, don haka ya kamata a nuna yabo gare ta, bisa tunanin ta na samun ci gaba tare da kiyaye muhalli, matakanta za su taimakawa duniya wajen farfado da lafiyar ta.
Kahwaji ya ce, tilas ne dan Adam ya yi kokarin kyautata dangantakar dake tsakaninsa da halittu, da mayar da duniya mai lafiya. A wannan fanni, kasar Sin tana kan gaba. Ya yi imanin cewa, Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga farfado da lafiyar duniya. (Zainab)

Exit mobile version