Ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani a baya bayan nan, wadda ta shafi matakan kasar na shawo kan bazuwar sinadarai dangin fentanyl a kasar Sin.
Yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma’ar nan, kakakin ma’aikatar cinikayya ta Sin, ya ce takardar ta fiyyace daukacin matakai, da gabatarwa mai zurfi game da matsayar kasar Sin, da tasirin matakanta na shawo kan bazuwar sinadarai dangin fentanyl ga kasashen duniya.
- Gwamna Dauda Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikatan Zamfara Da Sakatarori 12
- Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara
Ya ce takardar ta yi cikakken bayani game da yadda Amurka ta kakaba harajin kaso 20 bisa dari kan hajojin kasar Sin da ake shigarwa kasar, ta fakewa da batun sinadarin fentanyl, matakin da ko kadan bai dace ba, kuma mataki ne na kariyar cinikayya, da daukar matsayi na kashin kai da cin zali.
Kasar Sin na kira ga Amurka da ta gyara kurakuren da take tafkawa, ta kuma rika kallon batun wannan sinadari na fentanyl ta mahanga mafi dacewa da sanin ya kamata, ta kuma magance matsalar fentanyl da kan ta, ba tare da dorawa wasu laifi ba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp