Binciken da wasu Dattawan Arewacin Nijeriya suka gudanar, ya nuna cewa ‘ya’yan da aka haifa sakamakon fyade da ‘yan bindiga ke yi wa mata a yankunan Katsina da Zamfara sun kai rabin miliyan.
Dakta Bashir Kurfi ne, ya shaida haka a wata hira da ya yi da BBC, kan matsalar tsaro a yankunan arewacin Nijeriya, musamman Katsina da Zamfara.
- Sojoji Sun Ceto Wasu Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Birnin Gwari
- Yadda ‘Yan Kasuwar Kwari Ke Tafka Asara Saboda Ambaliyar Ruwa A Kano
Kurfi ya ce binciken da suka aiwatar cikin shekarun da aka kwashe ana yaki da ‘yan bindiga, ya tabbatar musu da wadannan alkaluma sakamakon rahotanni da suka tattara daga kauyuka.
Ya ce mata da dama na kawo korafinsu da kuma bayanai kan irin mutanen da suke yi musu fyade.
Yankunan Batsari da Dutsenma da Kankiya da Chiranci da Funtua, Safana da dai sauransu duk ana samun irin wannan matsala a Katsina.
Ya ce a baya kafin matsalolin tsaro sai motoci 20 zuwa 50 su je Kano a rana ko daga Sakkwato zuwa Kano ko kasashen makwabta, amma yanzu an daina, ‘yan kasuwa sun daina tafiya saboda hadari da ke tattare da hakan.
Har wa yau, ya bayyana yadda matsalar tsaron ta haifar da komawa baya ga ilimi, noma, zaman lafiya da asarar dukiyoyin al’umma mai tarin yawa.