Ali kiraji Gashua" />

Matan Kasar Sin Sun Ba Da Muhimmiyar Gudummawa Wajen Yaki Da Talauci

Matan Kasar Sin

A kwanan baya, ni da abokaina mun kalli shirin bidiyon “GUDUNMAWAR MATA A YAKI DA TALAUCI” da sashen Hausa na CMG ya tsara da kuma watsa a kafar talibijin na “Dadin Kowa” na kasarmu Najeriya. Yanzu ina son gabatar da ra’ayina game da shirye-shiryen bidiyoyi da suka gabatar. Da farko mun kalli shirin bidiyo game da gudumowar da mata suke bayarwa a yaki da alnobar fatara da talauci a a lardin Gansu inda Malam Murtala Zhang weiwei da malama Fa’izah Muhammad Almustapha suka yi kokari sosai mutuka wajen gudanar da ziyarar aiki a kauyekun da gamaiyar kungiyoyin mata suke sarrafa kayaiyakin yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummarsu.

A lardin Gansu mun kalli gonaki da tarin bishiyoyi da ciyayi da sauran shuke-shuke Kore shar abun ban sha’awa sosai mutuka. Amma kuma abunda ya kara bamu mamaki shine, yadda duk wani kauye da malam Murtala Zhang da malama Fa’izah Muhammad Almustapha suka kai ziyara yana da kyau sosai matuka tamkar birni. Domun agaskiya akwai kyawawan hanyoyi masu ban sha’awa sosai ga kuma tsarin gine-gine masu inganci da tsarin gini mai kyau sosai mutuka. A lardin Gansu mun kalli yadda mata suke bada himma wajen yaki da alnobar fatara da talauci ta hanyar gudanar da aiyukan sarrafa fusahar yin dinki a gundumarsu a karkashin jagorancin Shugabar kungiyar mata a gundumar wato madam Mashosho wanda kuma hakan ya faiyace hakikanin gudumowar da mata suke bayarwa a shirin gwamnatin kasar sin na yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin.  Babu shakka, wannan shirin bidiyo game da gudumowar da mata suke bayarwa wajen yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin ya gamsar da ni da masu sauraro game da gudumowar da mata suke bayarwa wajen yaki da alnobar fatara da talauci a lardin Gansu na kasar sin. Masamman ma abunda ya kara bamu mamaki shine yadda matan gundumar ke himmatuwa sosai mutuka wajen koyon fusahohi kala-kala na yin sana’ar yin dinki dan yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar yankunansu. Kana Kuma abunda ya kara bamu mamaki shine yadda gamaiyar kungiyoyin mata suke bada himma wajen bada gudumowa a yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar gundumarsu. A gaskiya shugabar mata ta bada muhimmiyar gudumowa a shirin bidiyon, masamman ma yadda malama Mashosho wanda ita ce shugabar mata a kungiyar mata a gundumar ke himmatuwa sosai matuka wajen raka malam Murtala Zhang da malama Fa’izah Muhammad guraren da mata suke bada muhimmiyar gudumowa wajen yaki da alnobar fatara da talauci ta hanyar gudanar da aiyukan fusahar saka tufafi da sauran kayaiyaki a gundumar Dungshang. Kamar yadda muka kalli shirin bidiyon, malama Mashosho ta kara bamu mamaki sosai matuka inda take gudanar da aikin shiga cikin gidajen mata a gundumar Dungshang tana rarrashin mata a gundumar Dungshang dan su amunce su yi aikin koyon fusahohi kala-kala na yaki da alnobar fatara da talauci a gundumar Dungshang dake a lardin Gansu na kasar sin.

Na kara samun wayin kai da kuma fahimta game da kokarin da kungiyoyin mata suke bada muhimmiyar gudumowa wajen koyawa mata sana’o’in saka tufafi da kuma sauran kayaiyaki, abun akwai sha’awa sosai matuka.

Kokarin da gamaiyar kungiyoyin mata suke yi wajen yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar yankunansu a lardin Gansu zai taimaka sosai matuka wajen yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar yankunansu. Domun agaskiya yadda gamaiyar kungiyoyin mata suke bada muhimmiyar gudumowa tare da maida hankali sosai mutuka ainun wajen yin dukufa a gudanar da aiyukan fusahar saka tufafi da kuma sauran kayaiyaki a gundumar Dungshang yana da kyau sosai mutuka ainun. Bayanda muka kalli shirin bidiyo game da gudumowar da mata suke bayarwa a shirin gwamnatin kasar sin na yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar lardin Gansu na kasar sin mun kuma kalli shirin bidiyo game da gudumowar da mata suke bayarwa a yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar lardin Sichuan na kasar sin.

Daga karshe ma lura da cewa, kokarin da gwamnatin kasar sin suke yi wajen tallafa wa gamaiyar kungiyoyin mata a gundumar Dungshang ya taimaka wa mata a gundumar Dungshang wajen samun nasarar kawar da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar yankunansu a gundumar Dungshang wanda ya burgeni da kuma abokaina da kuma masu sauraro sosai mutuka.

Daga bisani kuma, ni da abokaina mun kalli shirin bidiyo game da gudumowar da mata suke bayarwa a shirin gwamnatin kasar sin na yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin a lardin Sichuan na kasar sin. Agaskiya wannan Shirin bidiyo ya burgeni sosai mutuka kana kuma ya bamu sha’awa sosai matuka. Domun agaskiya mun ga yadda mata suke bada himma wajen wanzar da aiyukan fusahar saka tufafi da kuma yin jaka, takalma da tufafi kala-kala masu ban sha’awa sosai matuka. Babu shakka gani ya kori ji. Domun agaskiya yadda mata suke bada gudumowa wajen yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar yankunansu a gundumar Zhoaque ta hanyar kafa kananan kamfanunuwan sarrafa kayaiyakin yaki da alnobar fatara da talauci da kuma girka gamaiyar kungiyoyin mata masu fafutukar yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar gundumarsu ya faiyace hakikanin gudumowar da mata suke bayarwa a yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin kamar yadda muka gani a wannan bidiyo game da yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin. Babu shakka ni da abokaina da muka kalli wannan Shirin bidiyo tare da su mun gamsu sosai matuka da gudumowar da mata suke bayarwa a shirin gwamnatin kasar sin na kawar da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin. Domun agaskiya abubuwa da kuma kayaiyakin da muka gani mata suna dukufa a kai wajen sarrafawa dan yaki da alnobar fatara da talauci a gurare guda 5 da malam Murtala Zhang weiwei da malama Fa’izah Muhammad Almustapha suka kai ziyara ya bamu sha’awa da kuma mamaki sosai mutuka. Amma kuma abunda ya kara bamu mamaki da sha’awa sosai shine yadda mata suka kakkafa kungiyoyin mata a kowace gunduma da malam Murtala Zhang da malama Fa’izah Muhammad suka yi ziyara a dukkan yankunan guda 5. Kazalika Kuma, tallafi da goyan baya da gwamnatin kasar sin ke himmatuwa a kai wajen yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar wayannan yankunan guda 5 da gwamnatin kasar sin suka kaddamar da shirin yaki da alnobar fatara da talauci ya kara wa matan yankunan kwarin guiwar kawar da alnobar fatara da talauci sosai mutuka. Yadda mata suke bada himma wajen gudanar da aiyukan fusahar saka tufafi da kuma sauran kayaiyaki bisa kokarinsu na yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar yankunansu a dukkan yankunan guda 5 ya kara mana fahimta da kuma wayin kai game da kokarin da gwamnatin kasar sin suke yi na fatattakar alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kasar sin nan da karshen shekarar nan mai karewa ta 2020. Abubuwan da mata suke sarrafawa a dukkan yankuna da gundumomi da lardina da malam Murtala da malama Fa’izah suka gudanar da ziyarar aiki ya bamu sha’awa da burgewa da kuma mamaki sosai mutuka. Amma agaskiya kauyen karshe a ziyarar aiki da malam Murtala da malama Fa’izah suka yi wato kauyen Sanhe matan kauyen yan kabilar Yi sun burgeni da kuma abokaina da muka kalli wannan Shirin bidiyo tare da su. Domun agaskiya bayan kokarin da suke yi wajen yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kauyensu. Suna da san mutane, masamman ma bakaken fata ganin yadda suka amunce su yi wa malam Murtala da malama Fa’izah bayani dalla-dalla adangane da aikace-aikacensu na yaki da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kauyensu. Agaskiya matan kauyen yan kabilar Yi suna da kokari da hazaka mutuka wajen gudanar da aiyukan fusahar saka tufafi da sauran kayaiyaki domun su kawar da alnobar fatara da talauci a tsakanin al’ummar kauyensu na Sanhe. Dud da cewar, Sanhe kauye ne, amma yana da kyau sosai da kuma ban sha’awa sosai matuka.

 

 

Exit mobile version