Matar Gwamnan Bauchi Ta Kashe Miliyan 80 Don Horar Da Mata Sana’o’in Dogaro Da Kai

Kimanin naira miliyan tamanin ne aka kashe wajen horar da mata manya da kanana kimanin 1,600 sana’o’in dogaro da kawuka daban-daban da aka zakulosu daga mazabu sanatoci uku na jihar Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana hakan a bikin yayen matan da suka samu horon a gidan gwamnatin jihar Bauchi a Jiya.

Horaswar kan sana’o’in dogaro da kai din wacce uwar gidan gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar da hadin guiwar ma’aikatar mata na jihar ne suka dauki nauyin bayar da horon ga mataye dubu da dari shida domin samar musu da yanayin tsayuwa da kafafuwansu.

Muhammad Abdullahi Abubakar wanda mataimakinsa Injiya Nuhu Gidado ya wakilta ya ce gwamnatin jihar mai ci ta kirkiro da shirye-shirye daban-daban domin tallafa wa matan, da niyyar kawar da banbance-banbance da ake nuna musu wadda suke da alaka da zamantakewar yau da gobe na al’adance wadda suke durkusar da matan kan cimma muradunsu na rayuwa.

Ya yi bayanin cewar wannan dalilin ne ya sanya gwamnatin jihar ta kirkiro da wasu hanyoyin da suke da nasaba da rayuwa da kuma ci gaban matan wadanda suka kunshi samar musu da magunguna kyauta wa yara kanana da kuma mata masu juna biyu hade kuma da koya musu sana’o’in dogaro da kawuka domin tsayuwa da kafafunsu.

Gwamnan ya yi kira ga matan da su tabbatar da yin amfani da ababen da suka koya a lokacin horarsa gami da yin amfani da kudaden da suka samu domin yin amfani da su yadda suka dace domin samun hanyoyin dogaro da kai don kauce wa matsatsin rayuwa hade da inganta rayuwarsu.

A nata jawabin, jagorar shirya taron bita don horar da mata sana’o’i daban-daban na dogaro da kai din, Uwar gidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Muhammad Abubakar ta ce naira miliyan goma sha shida ne aka ware domin raba wa dukkanin matan da suka amshi horon a matsayin jarin da za su rika don ci gaba da riritawa.

Ta bakinta “sana’o’in sun hada da dinkin sabule da zanin gado, kayyakin kamshi na daki, sarrafa taliya, mangeda, da sauran kayyakin abin da ake sarrafawa domin mataye su dogara da kawukansu, dukka mun yi kokarin bayar wa mata horo kan wadannan fannonin domin taimaka wa rayuwarsu”.

Matar gwamnan ta kuma yaba da na mijin kokarin da gwamnatin jihar Bauchi take yi wajen taimaka wa shirye-shirye da kuma hanyoyin da suke taimaka wa mata hade da matan da suka rayuwa a karkara.

Tun da fari, sabuwar kwamishinan harkokin mata da bunkasa yara Hajiya Rukayya Ibrahim ta yaba da kokarin kananan hukumomi da suka samar wa matan guraben zama da kudaden zirga-zirga a dukkanin tsawon lokacin da kwashe ana horaswar.

Da suke jawabin godiya a madadin dukkanin matan da suka ci moriyar shirin Mariya Abdullahi da Bebin Malam sun yaba sosai da kokarin ofishin matar gwamnan Bauchi da ma’aikatar harkokin matan da suka bijiro da shirin domin taimaka musu sai suka yi amfani da wannan damar wajen bayyana cewar za su yi duk mai iyuwa wajen yin aiyukan da suka dace da ababen da suka koya domin tsayuwa da kafafunsu “mun koyi sana’o’I daban-daban, a madadin dukkanin matan da suka ci moriyar shirin muna mika godiyarsu sosai ga matar gwamnan Allah ya saka”. A cewarsu.

Horarwar wadda ya guda karkashin shirin tallafawa na matar gwamnan jihar mai suna B-SWEEP.

Exit mobile version