Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim, matar Sarkin Suleja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, ta rasu bayan doguwar jinya. Sanarwar rasuwar ta fito ne daga Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Abubakar Usman, wanda ya bayyana cewa Marigayiyar ta daɗe tana fama da rashin lafiya kafin Allah ya yi mata rasuwa.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa, SSG ya bayyana mutuwar Hajiya Rahmatu a matsayin babban rashi ga masarautar Suleja da kuma Jihar Neja baki ɗaya. Ya ce marigayiyar ta kasance uwa mai daraja, wadda ta ba da gudummawa wajen zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
- Tinubu Ya Tura Badaru Neja Kan Sace Dalibai Sama da 200
- Gwamnan Neja Ya Yi Allah-Wadai Da Sace Ɗaliban St. Mary A Papiri
Alhaji Usman ya jaddada cewa Hajiya Rahmatu ta rayu cikin tawali’u, da tausayi da hidima ga al’umma, musamman ta fuskar ilimi, inda ta kafa makarantar Rahma School a Suleja. Ya ce ta yi namijin ƙoƙarin wajen inganta tarbiyyar yara da bunƙasa ingantaccen ilimi a masarautar.
Gwamnatin Jihar Neja ta yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayiyar ya kuma bai wa Sarkin Suleja da iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.














