Wani matashi mai shekara 20 mai suna Umar Auwal, wanda aka fi sani da ‘Abba Dujal’, ya miƙa kansa ga rundunar ‘yansanda a Jihar Kano.
Ya amsa laifin kashe mutane da dama tare da satar babura da wayoyin salula a Kano da Jigawa.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 7 A Wani Sabon Hari A Benuwe
- Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya ce matashin ya bayyana kansa ne bayan da ‘yansanda suka ƙara matsa lamba wajen kai samame a maɓoyarsu.
Umar Auwal, mazaunin ƙaramar hukumar Wudil, ya ce ya daɓa wa wani mutum da ake kira ‘Boka’ wuƙa a Sabon Gari, sannan ya sace wayarsa ƙirar Infinix Hot 40i, wadda ya sayar da ita kan kuɗi Naira 40,000.
Ya kuma amsa cewa ya kashe wani mutum a unguwar Kurna, sannan ya sace wayarsa ƙirar Samsung S26, wadda ya sayar da ita kan kuɗi Naira 160,000.
Haka kuma a ƙaramar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa, ya amsa cewa ya kashe wani mutum sannan ya sayar da babur ɗinsa wanda ya sace a kan kuɗi Naira 300,000.
Rundunar ‘yansanda ta ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kansa a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), don tabbatar da gaskiyar iƙirarin da ya yi da kuma gano ko akwai wasu da suke tare da shi.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da matakin da Umar ya ɗauka na miƙa kansa, tare da kira ga sauran masu laifi da su kwaikwayi irin wannan mataki.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan za ta ci gaba da ƙoƙari wajen kawar da masu aikata laifi a faɗin jihar.
‘Yansanda sun buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp