A wata gagarumar nasara ta samar da Makamashi a Afirka, matatar Dangote da Neptune Oil sun yi hadin gwiwa ta fitar da Man fetur daga matatar mai ta Dangote (Babbar matatar mai a Afirka) zuwa kasar Kamaru.
Wannan nasara da aka samu sakamakon hadin gwiwa tsakanin kamfanonin biyu, ya jaddada kudirinsu na karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Kamaru tare da biyan bukatun makamashin da yankin ke bukata.
- Hukumar Hisbah Ta Kama Fiye Da Katan 200 Na Barasa A Sokoto
- Tinubu Ne Ya Fara Amanna Da Harkar Crypto Kafin Trump – Shugaban SEC
Aliko Dangote, Shugaba na rukunin Dangote, ya bayyana cewa: “Wannan farkon fitar da man fetur zuwa Kamaru, nuni ne na hangen nesanmu na zamowa daya domin kai ga Afirka ta zamo yanki mai cin gashin kansa a fannin makamashi.
“Tare da wannan ci gaban, mun aza harsashi, inda Afirka za ta rika ta ce albarkatun nahiyarta domin rarraba su a tsakanin jama’arta.”