Matatar man Dangote ta karɓi danyen mai ganga miliyan daya cikin miliyan shida daga hannun kamfanin mai na NNPC a ranar Alhamis.
A yanzu haka matatar na dab do soma tace mai da zarar ta kammala karbar ɗanyen mai daga NNPC.
Wannan dai na cikin yunkurin da Ɗangote ke yi na samar da wadataccen man fetur da samar da daidatuwar farashinsa kazalika da kuma samar da man a nahiyar Afirka ga baki daya, wanda wani yunkuri ne inganta tattalin arziki Nijeriya, kamar yadda Ɗangoten ya bayyana.
A makon da ya gabata ne dai kamfanin na Ɗangote ya karbi jirgi na hudu mai dauke da ganga miliyan ɗaya.
Ana sa ran mako mai zuwa za a kai sauran danyan man ganga miliyan daya wanda zai sa ya kai adadin miliyan shida idan aka hada da wanda aka kai wa matatar a baya.
Kuma da zarar an kammala kai man, kamfanin zai soma tace shi zuwa man fetur.