Matatar Dangote ta ƙaryata iƙirarin cewa ta sayar da man fetur ga kamfanin mai na Nijeriya NNPCL a kan Naira ₦898 kowace lita.
Wannan musayar yawun ya biyo bayan wata sanarwa da aka ce an jingina wa kakakin NNPCL, Olufemi Soneye, wadda ya tayar da hankulan ‘yan Najeriya.
- Kamfanin NNPCL Zai Cefanar Da Matatun Mai Na Kaduna Da Warri
- Matatar Man Dangote: Za Mu Shigo Da Mai Idan Kudin Sufurinsa Ya Fi Sauki Daga Waje -IPMAN
A wata sanarwa da babban jami’in hulɗar jama’a na rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar, kamfanin ya bayyana wannan zargi a matsayin ɓata suna da nufin rage martabar ci gaban da aka samu wajen magance matsalar makamashi ta dindindin a Nijeriya.
Kamfanin ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar, su kuma jira sanarwa daga kwamitin siyar da ɗanyen mai ga manyan matatun mai na cikin gida, wanda zai fara aiki daga 1 ga Oktoba, 2024. Chiejina ya bayyana cewa, ɗanyen man da kamfanin ke amfani da shi yanzu haka an saye shi ne da dala kuma ana siyar da shi ga NNPCL da dala, wanda duk da haka ke samar da ragi mai yawa idan aka kwatanta da man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
Sanarwar ta ba ‘yan Nijeriya tabbaci cewa kamfanin na da niyyar tabbatar da wadatar mai mai inganci a faɗin ƙasa, da nufin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin man fetur da aka daɗe ana fama da ita.