Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayyana cewa, ba za a sayar da matatar mai ta Fatakwal ba, inda ya jaddada kudirinsa na kammala cikakken gyare-gyare da kuma rike matatun man.
Shugaban kamfanin ne, Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana hakan a wani taro da aka yi a babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata.
- Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
- Ku Daina Kashe Mutane Ko Ku Miƙa Wuya – Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Bindiga
Ojulari ya bayyana cewa, wannan matsaya ba wai an sauya tsari ba ne, dama tuni tsarin kin sayarwar na nan, “An dan yi tsokaci ne game da ci gaban da ake samu na gyare-gyare a matatun Fatakwal, Kaduna da Warri.”
A cewarsa, binciken da ake yi ya nuna cewa, shawarar da aka yanke na fara gudanar da aikin matatar man ta Fatakwal kafin a kammala cikakken aikin gyaranta bai kamata ba.
Ya kara da cewa, duk da cewa an kokarta kan farfado da dukkan matatun man guda uku. Sai dai da dama na kira ga cewa, ya kamata a yi hadin gwiwa a fannin fasaha don kammala aikin gyaran matatar mai ta Fatakwal, amma sayar da ita, zai kara ruguza darajarta.
Wannan tsakaci ya zo ne biyo bayan rade-radin da ake ta yadawa bayan kalaman shugaban NNPC, Ojulari a taron OPEC na shekarar 2025 da aka yi a Vienna na kasar Ostiriya a farkon wannan watan, inda ya yi nuni da cewa “komai na iya faruwa da matatar” yayin wata hira da Bloomberg.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp