Mummunan harin da ake kai wa fararen hula da sunan ‘kuskure’ a Nijeriya na dada daukar hankali, inda al’amura ke kara kamari a ‘yan shekarun nan. Tun a shekarar 2017 da aka rika samun aukuwar hakan a yankin arewa maso gabas, har yanzu ba a magnace ba inda ko a baya-bayan nan, akalla fararen hula 40 aka kashe a garin Mutumji da ke karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara.
A wannan makon Nijeriya ta tsunduma cikin alhini yayin da akalla fararen hula 85 suka rasu bayan wani jirgin yakin sojoji mara matuki ya jefa bom a kauyen Tudun Biri da ke yankin Rigasa a Jihar Kaduna, yayin da al’ummar Musulmi suke gudanar da taron Maulidin Annabi Muhammad (SAW).
- An Kaddamar Da Cibiyar Buga Muhimman Takardu Ta AU Da Sin Ta Ba Da Taimakon Ginawa
- Jami’an NDLEA Sun Yi Artabu Da Miyagu A Jihar Edo
Baya ga wadanda suka rasu, akwai kimanin mutum 66 da suka jikkata a harin, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ta fitar a cikin wata sanarwa. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto an binne gawarwaki 85 da suka hada da yara da mata da tsoffi, yayin da ake ci gaba da neman karin wadanda abin ya shafa, in ji hukumar.
Domin neman ba’asin musabbabin wannan lamari, LEADERSHIP Hausa ta tattauna da wani kwararre kan harkokin tsaro a Nijeriya, Aliko Ibrahim El-Rasheed, wanda ya taba aiki a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, kuma tsohon jami’in tsaro na sirri kana hafsan sojan sama.
A cikin shirin D Space (twitter), da LEADERSHIP Hausa ta gudanar ranar 5 ga Disamba, El-Rasheed ya bayyana rashin kyakkyawan tsari na tattara bayanai da aiki da su a sassan rundunonin tsaro daban-daban da suka hada da sojojin sama, da na kasa, da na ruwa, da ‘yansanda, da jami’an tsaron DSS, a matsayin babbar matsalar da ke haifar da ire-iren wadannan hare-hare a kan fararen hula.
Ya kawo misalign abin da ya faru a sansanin ‘yan gudun hijira na Rann a shekarar 2017, da ke iyaka da Nijeriya da Kamaru, inda aka yi asarar rayuka sama da 100, El-Rasheed ya sake bayyana irin wannan lamarin da ya faru Zamfara a watan Disambar 2022, da irin asarar rayukan da aka rasa sakamakon hare-haren bisa kuskure.
Kamar yadda El-Rasheed ya bayyana, matsalar ta ta’allaka ce da gazawar jami’an tsaron Nijeriya wajen samar da hadin gwiwa a tsakaninsu. Ya kuma jaddada bukatar sojoji da ‘yansanda da hukumomin leken asiri su rika musayar bayanai ta ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaron kasa.
El-Rasheed ya kuma gano akwai wani babban gibi da ake samu a tsakanin jami’an tsaro da gwamnatocin jihohi wanda ya yi kiran magancewa, domin a cewarsa rashin hadin kai yana haifar da babban kalubale ga aiwatar da ingantattun shirye-shirye ko atisayen da aka tsara don hana irin wadannan abubuwan faruwa.
Yayin da yake kawo mafita kuwa, El-Rasheed ya zayyana muhimman abubuwa guda uku wanda ya kamata a kalla. Da farko, ya jaddada mahimmancin tabbatar da ingancin bayanai daga jami’an tsaro kafin a ba da izinin duk wani aiki ko atisaye.
Na biyu, ya jaddada bukatar inganta hanyoyin musayar bayanai a tsakanin dukkanin jami’an tsaron Nijeriya, da samar hadin gwiwa sosai da sosai a tsakaninsu.
A karshe El-Rasheed ya bukaci jama’a da su sanar da jami’an tsaro na kusa da su a lokacin gudanar da manyan tarukan al’umma, inda ya jaddada muhimmancin gudanar da taruka da rana kasancewar ana cikin yaki ne da ‘yan ta’adda, domin dakile sake faruwar lamarin.
…Muna Tattaunawa Da Gwamnatin Tarayya Kan Lamarin – Gwamna Uba Sani
Gwamna Jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, a lokacin da abin ya faru a cikin dare ya nemi shugaban rundunar tsaron Nijeriya Janar Christoper Musa, wanda dan asalin Jihar Kaduna ne ya nuna masa bacin ransa ganin irin ibtila’in da aka samu na rasa rayuka masu yawa haka.
Ya kuma bayyana cewa ya yi magana da Shugaban Kasa Bola Tinubu, “Muna nan muna daukar matakai, wadanda suke a asibiti, gwamnati za ta dauki nauyin yi musu magani, na kuma yi kiran cewa, lallai a yi bincike don sanin abin da ya kawo matsalar kuma duk wanda aka samu da laifi na kusukure a duba a gani in ganganci ne domin a dauki matakai saboda kar a sami irin wannan abin a nan gaba”.
Ya kuma ce, Sojoji ba a karkashin gamnatin jihar suke ba, mallakin gwamnatin tarayya ne, “Za mu jagorancin ganin an tabbatar da yin abin da ya kamata, amma wannan abu ne da ni kadai ba zan iya yanke hukunci ba dole sai mun zauna da shugaban kasar Nijeriya don sanin yadda za a fito wa batun biyan diyya, kuma na riga na yi masa bayani mun tattauna da shi, wajibi ne mu tsaya tsayin daka don kare rayuwar al’umma da dukiyoyinsu, za kuma mu tabbatar da ba jami’an tsarto dukkan hadin kan da suke bukata don samun nasarar yakar ‘yan ta’adda.
“Tuni muka fara taimakawa wadanda suka jikkata a asibiti da kuma iyalan wadanda suka rasu, ba mu jira agaji daga gwamnatin tarayya ba.” In ji shi.
…Ansariddeen Attajjaniyya Ta Gabatar Da Bukatu 5
Kungiyar Jam’iyyatu Ansariddeen Attijjaniyya ta lissafa wasu abubuwa guda biyar da take neman gwamnatin tarayya ta aiwatar bisa kisan kiyashi da jirgin sojojin Nijeriya ya yi wa masu bikin maulidi a kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.
Kungiyar ta bayyana abubuwan ne a wani taron ‘yan jarida da ta kira a shalkwatarta da ke Abuja.
Cikina abubuwan da kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya ta yi sun hada da gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa kan tare da sabunta bayanai ga al’umma, saboda tabbatar da adalci.
Haka kuma kungiyar ta ce dole ne a karfafa ka’idojin aiki a tsakanin sojojin Nijeriya, musamman ma na tura jiragen marasa matuKi.
Har ila yau, kungiyar ta bukaci a horar da sojoji sanin ‘yancin Dan’adam da kuma kare rayukan fararen hula tare da jaddada tausayawa da mutunta bambance-bambance da kuma fahimtar al’adu, wanda hakan na iya taimakawa wajen hana sake afkuwan wannan lamari.
Ta kuma yi kira da a samar da hadin kan a tsakanin sojoji da kuma al’umma.
Daga karshe, kungiyar ta nemi gwamnatin tartayya ta biya diyyar rayukan da aka salwantar ga iyalan wadanda lamarin ya shafa. Ta ce dole ne a tallafa wa rayuwar iyalan da suka rasa ‘yan’uwansu da kudade, domin sake rayuwarsu.
Da yake karin bayani, Babban Sakataren Kungiyar na Kasa, Alhaji Alkasim Yahaya ya bayyana cewa, “Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari. Babu wata magana da za ta iya rage radadin da suke ciki, amma za mu ci gaba da yin addu’o’i a gare ku.
“Muna bakin cikin yadda wannan musiba ta faru a daidai lokacin da al’umma ke bikin murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) cikin lumana. Muna kira da rundunar sojin Nijeriya ta gudanar da sahihin bincike kan lamari tare da daukan mataki ga duk wadanda aka samu da hannnu a ciki.
“A matsayinmu na kungiya, muna bukata a nuna gaskiya da rikon amana wajen hukunta wadanda suka aikata wannan kisan kiyashi. Mun san cewa babu wanda ya fi karfin doka, dole ne a hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa ga mabiyanmu ba tare da la’akari da matsayinsu ba,” in ji shi.
Kungiyar ta ce aikata wannan mummunan lamari ba karamin laifi ba ne na take hakkin Dan’adam, musamman a lokacin bikin zagayowar haihuwar Annabi (SAW) da masoya ‘yan Tijjaniyya ke yi duk shekara. Sannan kuma ta yi kira da rundunar sojin Nijeriya da gwamnatin tarayya da su gaggauta daukar mataki cikin gaggawa tare yin amfani da wadannan sharudda.
Ta ce a shirye take ta ba da goyon baya da hadin kai ga masu ruwa da tsaki domin kawo sauyi mai ma’ana da kwanciyar hankali a Nijeriya.