Ammar Muhammad" />

Matsalar Rashin Wutar Lantarki Na Kazancewa A Benuzuwela

Shugaban kasar Benezuwela Nicolas Maduro, ya bayyana matakin gwamnatinsa na soma aiwatar da tsarin kasaftawa yankunan kasar hasken wutar lantarki daya bayan daya saboda matsalar karancin wutar da baki dayan kasar ke fuskanta sama da makwanni 3.

Bayyana Wannan matakin dai ya zo ne jim kadan bayan da shugaba Maduro ya bada umarnin rage sa’o’in da ma’aikata ke yi a bakin aiki, da kuma rufe makarantun kasar saboda matsalar karancin hasken lantarki da ya kazance a kasar. Ci gaba da fuskantar matsalar ce ta sanya dubban ‘yan adawa gudanar da zanga-zanga a ranar Lahadin karshen makon da ya wuce a birnin Caracas.

Sau uku Benuzuwela ta fuskanci matsalar rashin hasken lantarkin a watan Maris da ya gabata, inda kuma yanzu haka, jihohi 20 daga cikin 23 dake kasar ne ba su da wutar lantarkin ciki harda babban birnin kasar Caracas.

Kungiyar injiniyoyin kasar ta Benuzuwela a baya-bayan nan sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, ma’aikatar samarwa da rarraba hasken lantarkin kasar na iya samar da mega watts dubu 5 zuwa 6 ne kawai na karfin wutar lantarkin, a maimakon megawatts dubu 34 da kasar ta saba samu a baya.

Yayin da shugaban kasar Nicolas Maduro ya zargi Amurka da hannu wajen haddasa matsalar, shi kuwa Jagoran ‘yan adawa mai samun goyon bayan kasashe 50, dake ayyana kansa a matsayin halastacce shugaba, Juan Guaido, ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da zanga-zanga ba kakkautawa har sai sun cimma burin kawo karshen shugabancin Maduro.

Exit mobile version