Connect with us

RIGAR 'YANCI

Matsalar Tsaro: Gwamna Bagudu Ya Kaddamar da Kwamitin A Kebbi

Published

on

Gwamnan Jihar Kebbi,Sanata Abubakar Atiku Bagudu a jiya ya kaddamar da Kwamitin bada shawara kan yadda zasu a magance matsalar tsoro a duk fadin jihar ta Kebbi wanda ake kira a turance ( Adbisory committee on community policing) bisa ga umurnin da sufeto janar na rundunar’yan sandan kasar Najeriya ya bayar da ga dukkan kwamishinonin ‘yan sandan jahohin kasar nan da su tabbatar da sun hada Kwamitin bada shawara kan yadda za a magance matsalolin tsaro a Jahohin kasar Najeriya baki daya a jiya a Birnin-Kebbi.

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya tabbatar wa Kwamitin cewar “ gwamnatin jihar Kebbi a shirye ta ke na bada gudumawar ta kan tabbatar cewa an magance matsalolin tsaro a jihar ta Kebbi da kuma kasarmu Nijeriya, Inji Gwamna Bagudu.”

Haka kuma ya bukaci mambobin Kwamitin da su zare damtse wurin bada shawarwari masu ingance da zasu sa a kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama dasu a Jahohin kasar Najeriya baki daya. Ya ci gaba da cewar” a shekaru biyu da su ka gabata hukumar kididiga ta kasa wato ( National Bureau of statistics) ta wallafa rahoton da ya nuna cewar jihar kebbi itace jahar da tafi kowace jaha kasar Najeriya zaman lafiya a matsalar tsaro.”

Saboda hakan zamu ci gaba da kara gwarin gwiwa ga harakokin tsaro a jihar da kuma sauran wasu Jahohin kasar nan domin tabbatar da cewa tsaro ya inganta. Hakazalika Gwmana Abubakar Atiku Bagudu ya ce “ tsaro a Jahohin kasar Najeriya na kowa da kowa ne ba gwamnatotin Tarayya da na jahohin bane kawai ba”. Saboda hakan yayi kira ga al’ummar jihar kebbi da kuma na sauran jahohin kasar nan da su ci gaba da bada tasu gudunmuwar su domin dakile matsalolin tsaro a Jahohin kasar nan.

Kwamitin da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya kaddamar ya hada da Kwamishinan ‘yan sanda jihar ta Kebbi CP Agunbiade OLuyemi Lasore a matsayin shugaban Kwamitin, Sarkin Gwandu, Muhammadu Iliyusu Bashar a matsayin shugaban na biyu ga Kwamitin sai kuma dukkan Shuwagabannin hukumomin tsaro a jihar a matsayar mambobin Kwamitin.

Sai kuma Babban Sakatare mai kula da harakokin tsaro a ofishin Sakataren gwamnatin jihar ta kebbi, Sufiyanu Garba Bena wato (permanent secretary security) a matsayin wakilin gwamnatin jihar.

Gwamna Bagudu ya kaddamar da Kwamitin bada shawara a kan harakokin tsaro a jihar kebbi a dakin taro na fadar gwamnatin jihar da ke a Birnin-Kebbi a jiya.

Shi ma a nashi jawabi wakilin sufeto janar na ‘yan sanda Nijeriya, DIG Abdul-Dahiru Danwawu mai kula da jahohin Arewa maso Yamma kan tsarin mulki da harakokin kudi a hedikwatar rundunar’yan sandan da ke a Abuja ya ce” nazo jihar kebbi ne domin tabbatar da cewar an kaddamar da Kwamitin bada shawara kan tsaro a jihar domin magance matsalolin tsaro wanda a kwanakin baya an kaddamar da irin wannan Kwamitin a jihar Sakkwato, haka kuma dukkan sauran jahohin kasar Najeriya za a kaddamar da wannan kwamiti don inganta tsaro a kasar nan, inji DIG Abdul-Dahiru Danwawu”. Ya kuma ce “ tsaro na kowa da kowa ne saboda haka Jama’a ne yanzu sune ‘yan sanda kansu da kansu a yankunan su da kuma kauyukansu domin sune su ka san dukkan mutanen da ke zama a garuruwansu, inji DIG”.

Har ilayau kara da cewar, “duk da yadda kididiga na tsarin bincike a rundunar’yan ‘yan sanda ya nuna cewar jihar kebbi tafi kowace jaha zaman lafiya a tsarin tsaro da kuma karancin rahotanin aikata laifufukan ta’addanci a kasar nan, inji shi”. Haka kuma yayi kira ga al’ummar jihar Kebbi da su ci gaba da taimakawa rundunar’yan ‘yan sanda da bayanan sirri kan abubawan da ke faruwa a yankunansu.

Daga nan ya godewa gwamnatin jihar da kuma al’ummar jihar kan irin goyon bayan da su ke bawai rundunarsa don ta kara inganta aikin ta na bada tsaro ga rayuwar al’ummar jihar da kuma dukiyoyinsu.
Advertisement

labarai