Gwamna Dauda Lawal, na Jihar Zamfara ya kaddamar da rundunar Sa-kai ta ‘Askawaran’ Zamfara, 2,046 a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara.
A jawabinsa , gwamna Dauda ya bayyana cewa, “Samar da tsaro yana daga cikin abin da na yi wa al’ummar Zamfara alkawari a lokacin yakin zabenmu ,yau gashi Allah ya nufe mu da kaddamar da rundunar ‘Askawaran’ Zamfara wadanda da zasu taimaka aa jami’an tsaro wajen kawar da ‘yan bindiga da suka addabi jihar nan.
- Ina Kiran Binani Da APC Su Mara Wa Fintiri Baya – Farauta
- Shari’ar Fintiri da Binani: Yau Jama’ar Adamawa Za Su San Matsayinsu A Kotun Koli
Da yardar Allah za mu yi iyakokarinmu tare da wadannan ‘Askawaran’ don ceto al’ummar Zamfara.”
A nasa jawabin babban bako, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa,wannan shiri na kaddamar da ‘yan sa-kai don fatatakar ‘yan ta’adda shiri ne na gwamnoni bakwai na yankin Arewa da yardar Allah sauran gwamnoni na jahohi na nan tafe,” in ji shi.
“Babu sulhu tsakaninmu da ‘yan vindiga sai fafatawa. Kuma yanzu gwamnan Zamfara ya tarbi yankinsa nima haka, wannan ya tabbatar da cewa lallai batun sulhu babu shi har abada sai mun ga bayan ‘yan ta’adda da yardar Allah.
Uban taro a wajen bikin Janar Ali Gusau, ya bayyana cewa, “An samar da rundunar ne don kare rayukanmu da dukiyoyinmu kuma bisa doka don haka za su yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro don samun nasara aikinsu.”