Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya bayyana matsalar tsaro da ake fuskanta a matsayin babban kalubale ga samar da abinci a kasar nan.
Babban jigon na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewar shawo kan kalubalen tsaro zai kawo karancin abinci.
- Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba A Fannin Raya Jiragen Masu Matukar Saurin Tafiya
- Abba Gida-Gida Ya Bai Wa Alhazan Kano 6,166 Kyautar Miliyan 65
Bafarawa, ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a ranar Litinin a Sakkwato.
“Kamar yadda muka sani, samar da abinci babban lamari ne a wanzuwar rayuwarmu, abin damuwa ne yadda a halin da ake ciki al’umma ba su iya zuwa gona su noma abin da za a ci.
“A yanzu haka, mutane da dama a karamar hukuma ta ba za su iya zuwa gona ba, wasu da dama sun gudu daga garuruwan su.”
Kamar yadda ya bayyana ta’addancin da ake fama da shi a yanzu a mafi yawan sassan kasar nan, zai zama tamkar wasan yara idan har karancin abinci ya kara ta’azzara.
“Yana da muhimmanci shugabannin kasar nan su sani matsalar tsaro ba wai ta tsaya kawai a ta’addanci ba. Matsalar karancin abinci ta fi muni kan ta’addanci,” in ji shi.