Matsalar Tsaro Na Barazana Ga Aikin Hanya, Mun Nemi Taimakon Sojoji – Minista Amechi

Ministan Sufuri

Daga Maigari Abdulrahman

 

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewar, ‘yan kwangilar da ke aikin hanyar jirgin kasa a Najeriya a wasu muhimman wurare sun bayyana fargabar su ta ci gaba da aiki sakamakon matsalar tsaro.

 

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyara ga sabon shugaban Sojoji, manjo Janaral Faruk Yahaya a Abuja. Ya kuma nemi taimakon sojoji kan samar da tsaro ga ma’aikatan jirgin kasar, wanda su ka nuna rashin amincewar ci gaba da aikin a halin yanayin tsaron kasar. Ma’aikatan dai sun hada da na kasashen waje da gida Najeriya.

 

A cewar sa, hanyar Fatakwal zuwa Maiduguri ce mafi barazana ga ma’aikatan, ya nemi agajin tsattsauran tsaro a hanyar yayin da ma’aikatan za su dawo aiki.

 

“Muna gab da cigaba da aikin Kano zuwa Abuja, amman ma’aikatan na matukar nuna tsoro da damuwa kan amincin su. Sun nemi mu nemi taimakon ku domin kula da tsaron su. Za’a fara aikin wannan watan, muna matukar bukatar ingantaccen tsaro daga gareku,” in ji Ministan

 

Ya ci gaba da cewa, “a cikin ma’aikatan akwai yan Najeria, kasar Sin, har ma da yan Fotugal, wanda za su fara aikin Kano zuwa Maradi daga wannan watan, akwai kuma yiyuwar fara aikin Fatakwal zuwa Maiduguri wanda shi ne ya fi barazana a gare mu”

 

 

Minsitan wanda ya ce ba su yi tunanin neman agajin soji ba a aikin hanyar Kano zuwa Maradi, to sai dai karuwar matsalar tsaro a kasar ya sa sai sun bukaci hakan.

 

A ci gaban jawabinsa, ministan ya nemi tashin Sojojin daga sansanin su na kasuwar Oshodi, Legas, domin samun kammala aikin hanyar, wanda tuni an biya kudin wurin, in ji Ministan.

 

 

Maimakon rubuta wasika, mun zabi mu ziyarce ku domin muhimmanci lamarin kuma zuwa da kai ya fi aike, in ji Ministan.

 

 

Da ya ke nasa jawabin, shugaban Sojojin, ya basu tabbacin shiga lamarin domin bada tsaro kamar yadda su ka nema.

 

Shugaban, wanda ya nuna rashin jin dadin na tashin rundunar daga sansanin tsawon lokaci, ya shaida masa cewar, rundunar za ta tashi daga sansanin su na kasuwar Oshodi, kodayake dai tashin runduna bayan sansani abu ne mai wahala da ke bukatar shiri da lokaci, in ji shi.

 

 

A bangaren sa, da yake maida magana, shugaban sojojin, General yahya, yayi alkawalin shiga cikin al’amarin, kuma ya bada tabbacin samar da tsaron da yan kwangilar suke bukata.

 

Da yake magana akan sojojinsu da suke kasuwar Oshodi yace, “Nayi mamakin da har yanzun bamu fice daga kasuwar ba, duk da nasan cewa wasu lokuta akwai wasu matsaloli dake sanya in munada sojoji a wani wuri, yanada wahala ya zama ace sun tashi lokaci guda ba, da wahala, ba kawai kamar kunnawa da kashe fitila bane”

 

Exit mobile version