Matsalar Tsaro: Wainar Da Aka Toya A Taron Gwamnoni Da Sarakunan Arewa

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

A jiya Alhamis ne masu ruwa da tsaki na yankin Arewa suka yi wani gagarumin taro a Kaduna, da nufin lalubo bakin zaren matsalar tsaron da ta addabi yankin da kuma irin barazanar tsaron da ‘yan asalin yankin ke fuskanta a fadin kasar nan.
Daga cikin wainar da aka tota a taron, shugaban kungiyar Gwamnonin Arewan, kuma Gwamnan Filato, Honarabul Simon Bako Lalong, ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne na masu ruwa da tsaki domin zakulo hanya ingantacciya da za su bi domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin baki daya.
Gwamna Lalong ya kara da bayyana cewa, daga cikin abin da suka tattauna a kai, sun hada da, matsalar tsaro da ta addabi yankin, da kuma cimma matsaya wajen ganin daukacin Gwamnonin Arewan sun samar da labukan shanu da gina wuraren kiwo domin samar wa ‘yan uwansu Fulani makiyaya wuraren da za su dinga kiwon shanu, don magance matsalar rikice-rikecen da ya dade yana faruwa tsakanin manoma da makiyaya na Yankin.
Gwamnonin Arewan sun kuma bukaci takwarorinsu Gwamnonin kudancin kasar nan, da su guji yin duk wani kalamai da zai kai ga tunzura al’ummar kasar nan cikin fitina, domin a cewarsu, Nijeriya kasar kowa da kowa ne, kuma dokar kasa ta bai wa kowane dan Nijeriya ‘yancin zama a duk inda yakeso, ba tare da muzgunawa da cin zarafi ba.=
A nashi bangaren, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa kungiyar Gwamnonin Arewa bisa irin matakan da take dauka na ganin ta kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin baki daya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, a yayin da ya wakilci shugaban kasa wajen bude taro kan matsalar tsaro da tattalin arziki da kungiyar Gwamnonin da Sarakunan Arewa suka shirya a Gidan Gwamnati na tunawa da Sir Kashin Ibrahim dake Kaduna.
Shugaban kasar ya kara da bayyana cewa, duk da irin Namijin kokarin da Gwamnonin Arewan ke yi, duk da haka, ya zama wajibi a gare su, da su kara tashi tsaye wajen ganin sun tunkari babban matsalar tsaron da yaki ci yaki cinyewa da ya addabi Al’ummar yankin baki daya.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana irin gudunmuwar da Gwamnatinsa ke bayarwa babu dare ba rana kan harkokin tsaro domin ganin an fatattaki ‘yan ta’adda dake cin karen su babu babbaka a Yankin na Arewa.
Shugaban kasan ya kara jaddada goyon bayansa ga duk wani mataki da Gwamnonin Arewan za su dauka domin ganin an kawo karshen matsalolin da ya addabi Yankin na Arewa. Sannan ya roki Gwamnonin Arewan da su hada hannu da sauran takwarorinsu na yankin kudancin kasar nan domin ganin sun shawo kan matsalar tsaron baki daya.
Shi ma a nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufai, ya bayyana cewa, yanzu ba lokaci ba ne na musayar yawu, ko korafe-korafe a tsakanin Gwamnonin. A cewar sa, al’ummar da suke mulka sun zura masu ido saboda nauyin hakkokinsu sun rataya a kan su shugabannin su, saboda haka ya zama wajibi a gare su da su yi mai yuwa wajen ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro da suke naima su addabi yankin nasu na Arewa.
Gwamna el-Rufai ya kara da bayyana cewa, a halin yanzu mutane na cikin tsoro da fargaba, mutane ba su da kwanciyar hankali, mutane ba sa iya bacci da ido biyu. Wanda a cewar sa ya kamata su hada hannu waje guda domin ganin an yi bankwana da matsalar tsaro a daukacin jihohin yankin na Arewa.
Taron na masu ruwa da tsaki na yankin Arewan, ya sami halartar wakilin shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, shugaban hukumar kula da harkokin tsaro ta kasa, Shugaban Rundunan ‘Yan Sandan Nijeriya Mohammed Adamu, daukacin Gwamnonin Arewa, Sarakunan a karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar III, kungiyoyin Dattawan Arewa, da sauran masu fada a ji daga yankin na Arewacin kasar nan.
Daga karshen taron, Gwamnonin da Sarakunan Arewa sun fitar da matsayarsu kamar haka;
Sun shawarci Gwamnatin Tarayya da lalle ta samar da kariya da ingantaccen tsaro ga duk makarantun da ke fadin Arewacin kasar nan.
Sannan sun kafa wani kwamiti wanda aka dora ma alhakin samar da wata gidauniya ta musamman domin tallafa ma wadanda ibtala’in rikici ya rutsa da su, da sake gina ma ‘yan gudun hijira dake yankin Arewa matsugunni.

Gwamnonin sun yarda za su hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen samar da Jami’an tsaro na cibilian JTF, domin taimaka ma sauran jami’an tsaro dake aiki a jihohin nasu.
Sannan sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajibi a hada kai da da kuma baiwa Sarakunan Gargajiya dama domin bayar da tasu gudunmuwar wajen inganta harkar tsaro a fadin kasar nan.
Sannan sun bayyana cewa, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tsaurara matakan tsaro wajen hana shigowa da muggan makamai ta ko ina a fadin kasar nan.
Sun bayyana cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta fitar da wata hanya da za a sami daidaituwa tsakanin manoma da makiyaya domin magance matsalar rikice-rikecen a fadin kasar nan.
Gwamnonin Arewan sun bayyana cewa, za su dawo da inganta harkar samar da ma’adinai a fadin Arewacin kasar nan, domin samun karin kudin shiga, da magance dogaro da man fetur.

Exit mobile version