Shafin da ke zakulo muku batutuwa da dama wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da matsalar da ke afkuwa wajen tarbiyyar da iyaye ke bawa yara.
Da yawan wasu iyayen na yawan aibata ‘ya’yansu da munanan kalamai wajen zagi da zarar ransu ya baci, musamman idan yaran sun yi musu laifi komai kankantar yaro.
- Yadda Muke Shagulgulan Bikin Babbar Sallah A Bana – Mabiya Shafin Taskira
- Halittar Mata Na Canzawa Bayan Aure
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko mene ne ribar hakan?, wadanne irin matsaloli hakan ka iya haifarwa ga yaran?, ko ta wacce hanya za a iya magance afkuwar hakan?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Princess Fatima Zahra Mazadu Jihar Gombe:
Toh dai abun fada anan wannan ba halin iyaye nagari bane ba, dan shi da tarbiyyar iyaye yake bi ya kuma tashi da shi, duk kyansa duk rashin kyansa, wanda ba za ka so kai na ka ya zamo wani iri a cikin al’umma ba, za ka ga mahaddatan kur’ani, ma’aikatan lafiya, sojoji da sauran ayyuka nagartattu, kai ko danka tsabar mugun baki da hantara, ya ki karatu sai shaye-shaye da neman mata, fashi da makami, sata, yin Sara suka da dai sauransu. Kai ba ka sakawa abun da ka haifa albarka ba, ta ya ya zai zamo nagari har ya zamo mai amfani?. Ba shi da riba ko kadan sai tarin bakin ciki da takaici, dan kullum su kansu iyayen kwana za su ke yi cikin zullumi, Gurbacewa, lalacewa, halaka, da susucewa. Shawara mu zamo masu sanya wa yaranmu albarka, ba namu ba ko na wani, dan mu ma watarana a samu masu sanya wa namu, kullum ka ke sakawa danka albarka akan abun da ya yi mai kyau ko mara kyau, Allah zai shirya maka shi ya daina munanan abubuwa. Sannan addu’a da kalma mai kyau, sannan a kara kula da su ta hanyar lallaba wa, Allah ya baka haihuwa ne dan ka tarbiyyar ba wai ka gurbatar ba. Furuci mummuna na iya hallaka kai kanka mahaifin dan ya zamo dan iska kai ma ba za ka tsira ba, saboda haka ba riba gurin munanan kalami ko magana ko furuci kan yaranmu, dan hatsari ne babba, kowa da ka gani nashi ya shiryu dauriya da hakuri ya sanya, ba wai dan ba a bata masa rai ba ko dan baya saba masa, amma in yana kau da kai yana addu’a da yawan sanya albarka shi zai sa dan ya zamo nagartacce abun alfahri.
Sunana Lawan Isma’il (Lisa) Jihar Kano Rano LGA:
Wannan sam! bai dace ba kuma ba tarbiyyar islama ba ce aibata da kuma zagi da munanan kalamai ga mutum ko da ma ba yaronka ba, musamman kuma iyaye ga yaransu wanda yake yin hakan kamar yi wa yara baki ne, shi ne ya sa muke ganin yara gashi mune muka haife su amma sune suke iya juya mu bayan tun suna yara an lalata rayuwarsu da munanan kalamai da kuma zagi. Bai dace ba sannan yara su ma za su iya tasowa da yi wa na kasa da su, daga baya kuma iyaye su zo suna son yaro ya daina bayan tun yana karami kayi masa ka kuma koya musu. Ba shi da riba balle ma har na kawo ribarsa domin gara ma ka kangarar da yaro da duka akan yawan aibatawa ko zaginsa. Yana bata tarbiyyar yara, yana sa su raina na sama dasu, yana koya musu munanan zage-zage kamar irinsu; Ashariya duba da yaro tun yana karami wasu iyayen suke danna musu ashar, da sauransu. Hanyoyin suna da yawa amma hanyar da ta fi dacewa ita ce kafin ka aibata yaro ko zaginsa ka tuna cewa yana lalata rayuwar yaro wanda yake kuma koda bayan babu rayuwarka to yaro zai zama ba nagari ba, don haka yaro koda ba namu bane mu tuna cewa nan gaba sune ginshikin al’umma, kuma dole ace dan gidan wane ne. Shawara su daina domin nan gaba ba zai taba haifar da da mai ido ba, kamar yadda na fada a baya yin hakan yana gurbata rayuwar yaro ne ko ba dan halak bane, Allah ya kiyaye mu ya kare mana zuri’a.
Sunana Sadiya Garba Umar Jihar Kano:
Wannan sam! bai dace ba, furta munanan kalamai ga mutum ko ba kai ka haife shi ba kuskure ne babba saboda baki kamar reza yake, kuma yana tasiri akan mutum, sannan bata taribiyyar yaranka ne su ma da haka za su tashi ba tarbiyya kowa za su iya gaya masa kalma mara dadi. Hakan ba shi da wani riba saboda karshe duk yaran da ya taso a karkashin irin wadannan mutanen wallahi za ki ga bai da tarbiyya, kuma komai girman mutum zai iya zaginsa tare da gaya masa maganar da bata dace ba. Hakan yana haifar da matsalar lalacewar tarbiyya da kuma jefa shi a halin ha’ula’i, domin wannan miyagun kalaman da ka ke kiranshi da su za su sa zuciyarsa ta bushe ya ji shi ma fa ya kai shege zai iya yin komai ba tare da wani fargaba ba. Ana iya magance wannan matsala ta hanyar gyara zamantakewa da iya sanin wanne irin kalami za ka yi ga mutum? ka san meye zai amfane shi nan gaba?, idan ka gaya masa ka san wanne ne zai rusa masa tarbiyyar da ka bashi. Shawara ta ga masu yin hakan shi ne su kasance masu tausasa lafazi ga yaransu idan suka ji yaransu suna zagin junansu ko suna fadan mummunar kalma a junansu to su yi musu fada su nuna musu hakan ba abu ne me kyau ba.
Sunana Ummu Maher (Mrs green) ‘Yar Mutan Kano:
Gaskiya wannan abin da iyaye suke yi ba su kyautawa, duba da irin matsalar da take cikin zagin yara, saboda tun a farko ka bata danka da bakinka, mai makon ka sanya masa albarka sai ka bige da aibata sa. Gaskiya hakan ba shi da wata riba, matsalolin da hakan ke haifarwa, shi ne; yana lalata yaro tun yana karaminsa tunda kin riga da kin lalatashi da bakinki, karshe kuma ki ce mutane ne suka aibatashi alhali kuma ke da kanki ki ka aibatashi. Hanyar da za a magance hakan shi ne; mu dinga kiyaye bakinmu da harshenmu tun ma kafin mu furta mummunan kalami ga yaro/yarinya. Shawara ita ce su dinga shiwa yaransu albarka a kullum, sai ka ga yara sun yi albarka wanda ke da kanki idan ki ka fito za ki san kin haifi mai albarka.
Sunana Auwal Ahmad Na’antu:
Hakika duk bacin rai bai kamata a dunga manta hankali ba, domin shi yaro dan kwaikwayo ne abun da ka ke masa to da shi zai tashi kuma ya yi a waje, domin zai zaci abun mai kyau ne. Babu wata riba a cikin haka sai asara, domin an gurbata tunanin yaron da ma tarbiyarsa, kuma shi ma zai je ya yi a gurin wasu yaran har su koya ka ga babu riba sai mummunar asara. Matsalolin suna da yawa, yaro zai taso baya shayin yin zagi a gaban kowaye kuma ba zai ga girman kowa ba indai ta gurin zagi ne, domin za ka ga yaran da iyayensu suke musu imbola za ka ga su ma da mutum ya yi musu abu za su bude hannu su yi masa, kuma zai zama wasu mutanan ba su da hakuri da zarar ya zagesu za su dake shi, ka ga nan ma an sami matsala domin yawan dukan zai sa yaron ya kangare ya daina jin zafinsa. Hanyar da za a magance hakan a ganina shi ne iyaye su dunga saita harshensu gurin yi wa yaro magana, sannan su san irin gidajen da dansu zai shiga na makota da kuma wanne yara zai dunga tarayya da su?, domin gudun fadawa matsala. Shawarata anan shi ne ina ga gaskiya duk iyayen da suke haka za ka ga rashin ilimi ne da kuma su ma sun taso a haka tun daga farkonsu, dan haka mutum ya san matar da zai aura, sannan ya fahimce ta in ya ga halinta ne haka to lallai ya dunga hanata, in ma mijin ne yake haka to matar ta dunga hana shi. Sannan dan Allah iyaye a dage da karatu domin yawanci karancin ilimi ke sa haka, kar ka ga ka girma ka ce wai kai ka wuce meman ilimi a’a ba a tsufa a nemansa, Allah ya shiga lamarin ya ba mu ikon aikata daidai.
Sunana Abbas Hassan Yalwa Jihar Bauchi Kandahar:
Gaskiya rashin ilimi ne yake janyo hakan, ba kowanne iyaye bane suke iya bai wa ‘ya’yansu ilimi da tarbiyya wanda za su tarbiyantar da nasu ‘ya’yan da zarar sun yi aure ba, shiyasa matsalolin iyaye akan ‘ya’yansu yake da yawa. Hakan ba shi da wani riba kuma ba shi da wani fa’ida kuma ba shida wani amfani ko na miskala zarratan. Domin bakin wani dan Adam ma guba ne ballantana ace bakin iyaye. Hakan yana iya harfar da lalacewar rayuwar yaro sakamakon bakin iyaye guba ce kuma zuma ce duk abin da suka roki Allah a kanka imma alkairi imma sharri ubangiji yana saurin karbar addu’a da zarar sun shiga cikin bacin rai akanka sai ka ga masifa, ballantana ace sun yi wani furuci akanka tabbas! rayuwar yaro tana sauyawa akan addu’ar iyayensa komai kyau ko mara kyau. Hanya 1 ce iyaye su kasance masu yi wa ‘ya’yansu addu’a a duk lokacin da suka tsinci kansu imma farin ciki imma bakin ciki, addu’a ita kadaice magani domin idan Allah ya shirya muku ‘ya’yanku farin cikin kune sakamakon addu’o’inku masu kyau, idan ‘ya’yanku suka lalace to bakin cikinku ne, sakamakon mummunar addu’arku akansu. Shawarar ita ce ku kasance masu hakuri akan ‘ya’yanku addu’a kadai tana raba ku da su, domin addu’arku nasara ce a gare su, sannan ku guji tilasta su akan abin da ba su so domin su ma suna da hakki a kanku. Nagartarku nasu ne nagartarsu na kune.
Sunana Imam Umar Kwasu Potaskum Jihar Yobe:
Bai dace uwa tayi munanan kalamai ga ‘ya’yanta ba, saboda bakinta yana tasiri ga yara. Babu riba sai kalubale da nadama a karshe, domin yaro zai fi karfinta. Hakan na haifar da Daba, Sata, da rashin Tarbiyya. Shawara hakuri da jawo yaro jiki wajan nasiha da addu’a. Hakuri za su yi su dinga yi musu addu’a.
Sunana Abubakar Sakeek daga Abuja:
Duk iyayen da suke haka su daina ba shida amfani, ko kadan babu riba sai dai janyo kara lalacewa ga yaron. Ya kan janyo yaro ya saba da zage-zage da kuma kara rashin jin maganar iyayensu, idan yaro ya bata maka yi musu addu’a ta fi zagi. Duk wanda yake yin hakan ya daina saboda babu riba sai dai kara lalata yaro a yawaita yi musu addu’a duk lokacin da suka yi ba dai-dai ba, sa’annan a yi musu fada da kar su kara hakan a nuna musu cewa sun yi ba dai-dai ba, dan kar su kara mai-maita hakan nan gaba.