Makarantu da dama a halin yanzu, ba su da kayan aikin da ya kamata a ce suna da su, musamman domin taimaka wa koyarwar ta kasance cikin sauki.
Haka nan, idan ana maganar darussan da suka shafi harkokin kimiyya da fasaha, makarantun da suke da wadannan kayan aiki har gara ma a ce ba su da su; sakamakon rashin ingancinsu.
- Yadda Wike Ya Kafa Tirihin Gudanar Da Ayyukan Ci Gaba A Abuja
- Badaƙalar Bashin Kaduna: Abin Da Ya Sa Ba Mu Gayyaci el-Rufai Ba – Hon. Lawal
Kazali, dakunan karatu babu littattafan zamani da mukalu da kuma mujallun da za su taimaka wa harkokin koyo da koyarwar.
Rashin tarbiyya na taimakawa wajen aikata magudin jarabawa, shiga kungiyar asiri, fyade da sauransu, wadanda ke taimakawa wajen gurgunta ci gaban ilimi.
Bincike ya gano cewa, akwai wasu cibiyoyin rubuta jarabawa; inda iyaye ke ba da kudi, domin ‘ya’yansu su samu sakamako mai kyau a jarrabawar kammala sakandare tare kuma da samun makin da ya dace, don samun cancantar shiga jami’a ko sauran makarantun da ke gaba da sakarandire.
Har ila yau, rashin kulawar iyaye shi ne babban abin da ya sa ake haduwa ko samun nakasu a bangaren ilimi. Domin kuwa, su ne garkuwa wajen kulawa da rayuwar ‘ya’yansu, musamman ta fuskar ba su tarbiyya da karatunsu da kuma sauran al’amuran rayuwarsu.
Akwai abubuwan da suke taimaka wa malamai wajen aikinsu na koyarwa, wadanda da ma da su ne suke amfani wajen jan hankalin dalibai; don mayar da hankalinsu kan abubuwan da ake koya masu.
Wadannan abubuwa sun hada da wadanda za su ji da na gani, littattafai, komfuta da sauransu, ba a samar wa malamai irin wadannan kayayyakin da za su taimaka musu wajen gudanar da aikinsu daga karshe, sai koyarwar ta zamar musu da wahala.
Babu wani tsarin ilimi da aka sama wa malamai, don yadda za su samar da ilimi mai nagarta ga dalibai, shi ya sa yawancin makarantu ba sa iya tafiya da tsari ko wani abu mi tasiri wanda zai yi kama da irin tsarin Kasar Ingila.
Ba kamar sauran sassa ko bangare ba, inda dalibai suke rubibin samun gurbinsu na makaranta, sai dai shi sashen ilimi da kuma kwalejin ilimi ba kowa ne yake son ya karanta bangaren ilimin ba, domin ya san maganar koyarwa ce.
Wani binciken da aka yi a shekarar 2015, na wadanda ke son shiga jami’oi; an samu kasa da kashi biyar daga cikin 1, 700,000 na wadanda suke son sashen ilmi, ba don komai ba sai don ba su da sha’awar yin aikin koyarwa.
Rashin tsare-tsaren aikin koyarwa masu nagarta yasa kwararrun da suka karanta sashen koyarwa, suka koma wasu wuraren da ake kula da hakkin ma’aikata daidai gwargwado, ko shakka babu irin hakan ne ke sa su ki maida hankalinsu kamar yadda ya dace ga lamarin aikin nasu na koyarwa.
Batun mafi karanci albashi a Nijeriya a lokacin da yana Naira 18,000, zai yi matukar wuya ga masu iyali su iya tafiyar da gida kamar yadda ya dace, kamar a bangaren tura ‘ya’yansu makaranta, saboda tsadar kudin makarantar da na littattafai da dai sauran makamantansu.
Littattafan da suka dace su rika taimaka wa dalibai wajen kara fahimtar abubuwan da ake koya masu, abu biyu ne a nan; na farko ko dai su kasance suna da wuyar samuwa ko kuma akwai dan karan tsada, ga su daliban ko malaman su saya su yi amfani da su.
Da Zarar an gano dalilan da suke sa ake samun matsaloli, duk abin da ake hange bai wuce a samu maganin matsalolin ba tare da bata lokaci.
Wannan dalili ne ya sa Johnson Olawale ya samar da hanyoyin da za a yi amafani da su wajen magance matsalolin da suke shafar ilimi a Nijeriya.
Matakin farko da ya dace a yi amafani da shi wajen kawo gyara kan matsalar ilimi a Nijeriya, wukar da naman na hannun gwamnati. Da akwai bukatar daukar matakai wadanda suka dace kasancewar su dole sai da su lamarin zai gyaru, idan har ana fatan a samu ceto sashen na ilimi.
Gwamantocin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi, akwai bukatar su kara zage damtse, don ganin sun daidaita tare da gyara matsayin ilimi ya kasance a matsayin iri daya da na sauran kasashe.