Connect with us

KIWON LAFIYA

Matsalolin Shaye Shayen Miyagun Kwayoyi A Nijeriya

Published

on

Shan miyagun kwayoyi zama ruwan dare a tsakanin al’umma musamman ma matasa maza har da ma mata, masu aure da wadanda ba su da shi. shaye-shaye na nufin duk wani yanayin da bil’adama zai sa kan shi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarin shi ta yadda ba zai iya bambanta ya kamata da akasin hakan ba.
Shaye-shaye na zuwa ne a yayin da mutum ya afka cikin shan kwaya sabanin yadda aka kayyade a sha shi, ko kuma shan giya ko tabar wiwi da dai sauran nau’ukansu wadanda za su bugar da mutum ko su kai shi ga maye.
Tabbatas!! shan miyagun kwayoyi kamar shan hodar iblis ta koken da hiroin suna kama mai amfani da su kai tsaye.
Sai dai abin ba haka yake da sauki ba, domin wasu gwaje-gwaje masu sauki da aka yi a cikin shekara talatin da ta gabata sun bayar da bayanai na daban.
Miyagun kwayoyi na da ban tsoro, kamar yadda hiroin da koken suke sa mutane su ji tsigar jikinsu ta tashi.
Ba wai alaka da manyan laifuka da illa ga lafiya ba kadai ne abubuwan da ke sa a kyamaci wadannan abubuwa hatta yadda suke zubar da kima da mutuncin mai amfani da su abin dubawa ne.
Ganin yadda shan wadannan miyagun kwayoyi ke raba mu da hankalinmu tare da hana mu tafiyar da harkokinmu bisa tasirinsu.
Duk lokacin da mutum ya fara amfani da wata muguwar kwaya to abin ya kama shi ke nan yadda zai sauya masa tsarin kwakwalwarsa, tun daga lokacin matashi zai fara Shiga babbar Matsala ta hanyar wulakanta addininsa. Idan har akwai abin da zai sake tsarin kwakwalwar mutum bai wuce shan mugwayen kwayoyi ba.
Amma dai duk da haka nazarin ya nuna cewa bayani ko yardar da iyaye suka yi cewa shan miyagun kwayoyi yau da gobe na sa a kamu da dabi’ar shan kwaya tun da farko, magana ce da aka yi watsi da ita yanzu ta zama gaskiya.
Abin da zai sa ta’ammali da miyagun kwayoyi ya kama mutum, har ya zama jiki a wurinsa ya wuce abin da aka gani a kwaya daya ko wasu kwayoyi komai karfinsu kamar koken da hiroin.
Zabin da kake da shi na kwayoyin wanda yanayin mu’amullarka da kuma muhallinka ka iya yin tasiri a kai, na taka muhimmiyar rawa kari kuma da irin matukar dadin da mai amfani da kwayar yake jin cewa yana samu, duka wadannan abubuwa ne da za a yi la’akari da su.
Ga masana tunanin ‘dan adam, ina ganin cewa ko a kan maganar kamuwa da dabi’ar amfani da miyagun kwayoyin za a iya amfani da nazariyya ta binciken wasu abubuwan ba sai lalle a ce sai wadda ta shafi kwayoyi ba kadai.
Hukumomi da kungiyoyin da ke yaki da shan miyagun kwayoyi a Nijeriya sun koka dangane da karuwar kwankwadar kwayoyi tsakanin matasa da matan aure suke yi.
Dangane da karuwar matasa da ke lalacewa da matsalar tabun hankali saboda shaye-shayen abubuwan da ke rikirkita masu kkwakwalwa na zamani da kuma hade-haden wasu sinadiran da ke chaza masu kai, haka babbar barazana ce ga makomar Nijeriya.
Ya zama dole da shugabanni da hukumomin tsaro su tashi tsaye tare da nuna bacin ransu ga matsalar da ta janyo karuwar matasa mashaya a cikin al’umma da suke taimaka wa wajen tayar da zaune tsaye a cikin kasa.
Saboda haka akwai bukatar dakile safarar kwayoyin da matasa ke amfani da su.
Malaman addinai da kungiyoyin matasan unguwanni su fara kaddamar da hari tare da gargadi ga masu sayar wa da shagunguna na chemist da shago-shago, wajen daina sayar da maganin tari ga matasa, da wasu matan aure, matukar dai in ba da takardan umurni ni ba daga wurin likita, domin rage sayar da maganin tari ga mashaya.
To sai dai abin ba haka yake da sauki ba, domin wasu masu sayar da kwayoyin suna da uwa a gidin murhu.
Miyagun kwayoyi na da ban tsoro. Kamar Benelin da ruwana kodin da koken kadai na sa marasa fara jin tsigar jikinsu ta tashi.
Bayan hubbasar gwamnati a matakai daban-daban wajen hana fasa-kwabrin kwayoyin, har ila yau ya zama dole iyaye su tashi tsaye wurin kula da tarbiyyar yara da matasa, sannan su dinga kula da harkokin yaransu na yau da kullum, su kuma kula da irin abokan da yaransu suke hulda da su. Dole ne sarakuna da malaman addinai su ma su tashi tsaye wurin tsawatarwa da fadakar da al’umma bisa illar shaye-shaye ta mahangar addini da rayuwa. Haka kuma al’umma su ba da hadin kai wurin taimakawa jami’an tsaro da jami’an yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi wurin gudanar da ayyukansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: