A ranar Juma’ar da ta gabata, da dare, dandazon jama’a daga sassa daban-daban na kasar nan suka yi tururuwa domin halartar zaman Maulidin Manzon Allah (SAW) wanda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group bisa jagorancin Sheikh Isma’ila Umar Almaddah (Mai Diwani) suka shirya, a zawiyyarsu da ke titin Matazu, kusa da titin Kagoro, a Unguwar Sabon Garin Tudun Wada da ke Kaduna.
Maulidin na bana wanda aka fara gabatar da karatuttukansa a zawiyyar tun daga ranar 1 ga watan Rabi’ul Awwal, an shafe tsawon daren 12 ga wata ana gabatar da shi inda aka kammala tare da gudanar da sallar Asubahin ranar Asabar.
Har ila yau, a bana Maulidin na Ahlul Faidhati Mai Diwani Group ya hada da yaye daliban zawiyyar wadanda suka haddace Alkur’ani mai girma, da suka hada da Muhammad Lawal Ibrahim, sai ‘ya`yan Sheikh Isma’il, Fatima da Khadija.
Wakazalika akwai mazajen da suka haddace Diwanin Shehu Ibrahim Inyass na yabon Manzon Allah (SAW) mai kunshe da baitoci sama da 4,000, da su ma aka yaye a zaman maulidin, su ne Nasiru Muhammad Gusau da Ibrahim Abubakar. Bugu da kari, akwai Shehul Hadi Mika’il wanda shi ma ya haddace Babban Littafin Ma’arifa na Shehu Ibrahim, Sirrul Akbar, sai sauran malaman makarantar Ahlul Faidhati Academy bisa jagorancin Malam Ahmad wadanda su ma aka gabatar da su domin murna da farin ciki da kuma godiya.
Maulidin wanda ya fara gudana bayan bude taro da addu’a daga Limamin Masallacin Ira na titin Kagoro da karatun Alkur’ani mai girma daga Malam Ahmadu, ya kunshi gabatar da karatun Littafin Nurul Basr da na Faidhul Ahmadi duka na Shehu Ibrahim wanda ya rubuta a kan tarihin Manzon Allah (SAW), sai kuma jawabai na ta’aliki da aka gabatar da harsuna daban-daban kamar Fulatanci, Turanci, Ebiranci inda mai gabatarwa da harshen Faransanci bai samu dama ba saboda kurewar lokaci.
Da yake gabatar da jawabin bude taron maulidin, Sheikh Isma’ila Umar Almaddah ya yi godiya ta musamman ga duk wadanda suka bayar da gudunmawa ta aljihu ko ta jiki domin samun nasarar maulidin, yana mai cewa, kowa Allah ya ga abin da ya yi kuma shi zai saka masa.
Tun da farko, kafin fitowa filin taron maulidin, Sheikh Isma’ila Mai Diwani ya yi wata ‘yar kwarya-kwaryar tattaunawa da manema labarai a game da abubuwan da maulidi ya kunsa da kuma irin darussan da ake koya a maulidin. Haka nan ya tabo batutuwan da suke faruwa a kasa kamar batun zaben 2023 da ke tafe da kuma ibtila’in ambaliyar ruwa da ke aukuwa a bana wanda ya yi addu’ar Allah ya mayar da fiye da abubuwan da aka rasa.
Sheikh Isma’ila ya fara ne da cewa, “Asslamu alikum ‘yan’uwa mun gode wa Allah da ya maimaita mana wannan rana ta haihuwar Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam, Rahmar Ubangijinmu ga duk halitta baki daya, wanda Allah Ta’alah ya fada masa ba don shi ba da bai halicci komai ba, yana daga cikin kirarin da ake wa Manzon Allah, ma’abocin shugabancin ba don komai ba, wanda Allah ne ya fada masa, kuma Baihaki ya kawo wannan Hadisi a cikin Dala’ilun Nubuwwa, kuma dama ya ce ba zai kawo hadisin ba sai a cikin ingantattu.
“To mun gode wa Allah da ya kawo mu wannan rana, domin wannan rana idan ta zo dukkan bayin Allah wadanda ya datar da su yau fiye da shekara dubu tun daga karni na hudu, bayin Allah sarakuna da malamai, da dukkanin masoya Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallama suna bikin raya wannan rana saboda alherin da ya sauka.
“Ubangiji madaukakin sarki ya fada mana a cikin Kur’ani, “Fazakkirhum Bi ayyamillahi” ka tunasar da su kwanakin Allah. Allah Ta’alah yana horon a tunasar da mu bayinsa kwanakinsa. Malamai suka ce ma’anar kwanakinsa su ne ni’imomin Allah. Kwana kwano ne, duk kwano, kwano ne sai abin da aka zuba cikin wannan kwanon, ma’anar tunasar da mu kwanakin Allah shi ne a tunasar da mu ni’imomin da ya yi a cikin wadannan kwanaki.
“Ni’momin Allah suna da yawa wadanda ya yi mana a cikin kwanaki, ga ni’imar samun Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallama, ni’imar Musulunci, ni’imar saukar Kur’ani, ni’imar Isra’i da Mi’iraji, ni’imar Sallah da muma muke ganawa da Ubangiji Tabaraka Wa Ta’ala a cikinta, da ni’imar Hijira, da ni’imar ranar Badar wacce da ita ce Allah ya daukaka Musulunci ya kaskanta kafirci, da ni’imar Fat’hu Makkata, yadda aka bude Makkah inda daga nan kuma duk garuruwa suka rika buduwa, da ni’imar cikar Alkur’ani din “Alyaumu akmaltu lakum dinakum, da ni’imomi da yawa wadanda za su wanzu har zuwa ranar tashin Alkiyamah, Allah ya ce a tunasar da mu wadannan ni’imomi don mu dinga gode wa Allah,” in ji shi.
Sheikh Isma’ila Mai Diwani, ya nunar da cewa ni’imar samuwar fiyayyen halitta, Annabi (SAW) ta dara duk wata ni’ima, yana mai cewa “Wadannan kwanaki da ni’momi suka sauka a cikinsu gaba daya, dukkansu suna bin ni’ima ce guda daya, ni’imar samuwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa sallam. Da Allah Ta’alah bai shirya addinin ba da bai samar da Manzon Allah ba, da bai shirya Kur’anin ba da bai samar da Manzon Allah ba, saboda Allah Ta’alah ya hukunta Kur’anin nan a hannun Annabi Muhammadu zai sauka, babu wanda ya isa karbe shi in ba shi Manzon ba, saboda mafificin litattafan Annabawa ne duka, don haka mafificin ma’aika ne zai iya karbar sa duka.
“Duk sauran littattafai ma na Allah ne, amma da ya zo a hannu shugaban halitta sai ya zama mafifici ne, don haka Allah ya ce a tunatar da mu wadannan kwanakin, “ in ji Shehun Malamin.
Sheikh Isma’ila Mai Diwani, ya kara da cewa, “Malamai sun tafi kan cewa, daren da Manzon Allah ya sauka ya fi daren Lailatul Kadri duk girman Lailatul Kadri. A daren na Lailatul Kadri kowannenmu Musulmi Allah yana ba shi daga falalarsa kyautar shekara 83 a duk shekara, shi ne wata dubu, wata dubu zai baka shekara tamanin da uku da ‘yan kadan. To mene ne ke sauka a wannan dare na Lailatul Kadri? Mala’iku ne suke sauke da Mala’ika Jibrilu Alaihis salam, shi ma Mala’ka ne amma saboda girmansa yana wata daraja daban da tasu.
To a nan malamai sai suka ce, idan muka duba kyautar da Allah ya ba mu ta Annabi (SAW), ta duniya ce gaba daya, to Manzon Allah mun samu alherin duniya da na lahira ne da shi, kun ga ashe ba za a hada alherin shekara tamanin da alherin da ba shi da adadi ba, sannan daren da mala’ika ke sauka a Lailatul Kadri da Jibrilu ba za a hada shi da daren da Manzon Allah ya sauka ba, wanda akwai managartan muminai da suka fi mala’ika a wurin Allah ballantana kuma shugaban muminan Annabi Muhammadu, Sallallahu alaihi wa sallam”, in ji Shehin.
Ya ci gaba da cewa, malamai sun ce idan Allah ya yi wa mutum ni’ima ta aure ko ta ‘ya’ya ko ta samun aiki ko ta cin jarabawa, ko kuma duk wani alheri da ya zo masa a rayuwarsa, ba laifi duk sanda wannan rana ta zagayo ya yi wani abu da zai nuna wa Allah ta’alah godiyarsa saboda wannan ni’imah da Allah ya yi masa, “tun da gashi Allah ya fada mana a cikin kur’ani mutanen Annabi Isa Hawariyawa sun ce suna so Allah ya saukar musu da abinci daga sama, Annabi Isa ya yi addu’a Allah ya saukar da abinci, ya ce Allah ka saukar mana da abinci daga sama za mu rike shi ya zamar mana Idi a gare mu, wato ranar murnarmu ranar godiyarmu.
Cikin godiyar Allah, ga shi addini ma ya taya su murna, Allah ma ya taya su murna, tun da ga shi sura ce guda Allah ya saukar Suratul Ma’idah, surar kabakin abinci, ma’ana surar da Allah ya saukar musu da abinci, to ina ga saukar Annabi Muhammad Sallallahu alihi wa sallam.”
“Mun gode wa Allah, muna daukar darussa daga maulidi, muna karanta baituka na yabon Manzon Allah, muna karanta wa kanmu tarihan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, mukan fadi hakurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallama, da kyawawan dabi’unsa da hankalinsa, da gudun duniyarsa, misali, zai ba wa mutane kyautar riga ta zinare ma, amma shi shugaba Sallallahu Alaihi Wasallama ya zauna ba shi da ita. Duniya tana zo masa amma sai ya rabar da ita.
An taba kawo Dirhami dubu casa’in daga Bahren su ne kudi mafi yawa da Manzon Allah ya taba gani, amma ya sa aka shimfida tabarma a masallaci aka zuba su ya dinga rabon su, Abbas Baffansa ya zo ya ce, to dan dan’uwana ka ga a Badar duk na bayar da dukiyata a fansar kaina da fansar ‘ya’yan dan’uwana guda biyu, to tun da kudi sun samu ka mayar min da abin da na rasa, ka mayar da ni talaka.
Manzon Allah ya ce debi, ya shimfida wani mayafi ya-diba-ya-diba, kudi koyins ba na takarda ba nauyi ne da su, ya daure ya kasa dagawa, ya ce da Sahabbai su taya shi, Manzon Allah ya ce a’a, dauki iya karfinka, a haka ya hada da bango da cinyarsa ya dauka, Ma’aikin Allah yana kallonsa yana murmushi yana mamakin tsoho irin wannan yana son kudi, haka nan Manzon Allah ya rabar da kudin nan gaba daya sai Dirhami biyu kawai suka rage ko shida ba a samu wanda zai karbe su ba, Ma’aikin Allah ya danka a hannun wata daga cikin matansa ya ce ko wani ya zo a bashi, da ya kwanta ya yi, ya yi bacci ya zo masa ya kasa.
Sai ya ce mata kin san abin da ya hana ni bacci kuwa, ai Dirhaman nan ne suka hana ni bacci, don haka a fita da su a je ko waye a kai masa. Daga nan ya samu ya yi baccin saboda gudun duniya.”
Sheikh Isma’ila Mai Diwani ya ci gaba da bayyana irin kyawawan dabi’un na Manzon Allah, in da ya ce, “Duk duniya ta yarda cewa shi mai gaskiya ne kuma kwararre ne, Allah ya taimake shi ya ci nasara wajen gyara zamaninsa, kuma Musulmi sun ci nasara cikin gyaran gabaki daya. Don haka mu koma wa musuluncin nan namu, mu koma kan kyawawan dabi’un nan namu, kuma mu koma koyi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallam, duk wata wayewa da ba koyi da manzon Allah ba ce sai ka ga hauka ne da wauta, ko da yake mai yin ta yana ganin yin ta wayewa ce.”
A karshe shehin Malamin ya yi addu’ar ga kasa da dukkan al’ummar Musulmi da ma duniya baki daya, in da ya ce “Muna fatan wajen Allah albarkar wannan rana, Allah ya biya bukatunmu, ya kiyaye imaninmu ya kiyaye kasarmu, ya kawo mana alherai, Allah ya biya bukatunmu. Wannan makami da ake yi wa duniya barazana da shi Nukiliya, Allah ka yi riko da hannunsu Allah ya tsare, domin duniya ta Allah ce babu wanda ya isa ya halaka duniya lokacinta da bai yi ba, amma kuma a iya shan wuya, ko wani burbudinsa ko kurarsa, ka da ka dauka idan ba a je fa inda kake ba za ka ce ai ni ba a Rasha nake ba ko Yukiren, a’a, abin game duniya yake.”
“Annabi (SAW) ya ce fitina a kwance take Allah ya tsine wa mai tayar da ita tun da ba mutum daya za ta shafa ba, to muna rokon Allah ya yi maganin lamarin, Allah ya datar da mu. Kuma ga siyasa nan tana kawo kai, Allah ka ba mu shugabanni nagari, Allah ka yi riko da hannunmu.
Allah mun tuba, Allah mun tuba, Allah laifinmu ne, Allah ka datar da mu. Gidan Rediyon Nijeriya Kaduna (FRCN), da AIT, KSMC, Trust TV da jaridar LEADERSHIP, duka Allah ya saka musu da alheri, Allah ya kawo hanyoyi na wayar da al’umma. Mun gode, mun gode, mun gode. Allah ka kara mana son addininmu, ka kara mana son Annabinmu Sallallahu Alaihi Wasallama.” Ya bayyana.