Wani makami mai linzami mai cin dogon zango da ‘yan tawayen Houthi na ƙasar Yaman suka harba ya dira a tsakiyar ƙasar Isra’ila, wanda ya haddasa gobara, amma ba a samu hasarar rayuka ba, kamar yadda rundunar Sojin Isra’ila ta sanar.
Hotunan da aka wallafa sun nuna gutsuttsura makami mai linzamin da ya sauka a kan wata tashar jirgin ƙasa a garin Modiin.
- Trump Da Harris Sun Caccaki Juna A Muhawara
- Sakon Da Aka Isar Game Da Yanayin Tekun Kudancin Kasar Sin Daga Wasu Taruka Uku
Magen David Adom, ma’aikacin agajin gaggawa a Isra’ila, ya ruwaito cewa mutane tara sun samu ƙananan raunuka yayin da suke neman mafaka.
Kamfanin dillancin labaran Saba na Houthi ya yi iƙirarin cewa makami mai linzamin ya kaucewa tsarin tsaron Isra’ila, wanda suka daɗe da neman keta shi.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya mayar da martani yayin wani taron majalisar ministocin ƙasar, inda ya yi gargadin cewa “ya kamata ‘yan Houthis su san cewa za mu ɗora farashi mai yawa kan duk wani yunkurin cutar da mu,” a cewar wata sanarwa daga ofishinsa.