Tsohon Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Kasa, Hon. Yekini Nabena, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya amince da mayar da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) zuwa yankin Neja Delta.
Ya kuma bukaci Tinubu da ya mayar da ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya zuwa jihar Binuwai inda amfanin noma ke da yawa don yin daidaito kan kudirin mayar da wasu sassan babban bankin Nijeriya (CBN) da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa FAAN daga Babban Birnin Tarayya (FCT) zuwa Legas.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta nuna sha’awarta na maida wani bangare na CBN da FAAN zuwa jihar Legas, ta ce, hakan zai fi da cewa. Duk da cewa, yunkurin ya jawo mahawara mai zaifi na daga goyon baya da adawa, musamman daga bangaren Arewacin Nijeriya.
Nabena, wanda ke zargin munanan manufar yin irin wannan yunkuri, ya ce, Shugaba Bola Tinubu tuni dama bai yi imani da kasancewar Nijeriya a matsayin kasa daya ba kafin ya zama shugaban kasa.
Jigon na APC a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba, ya nanata cewa, hukumomin tarayya alamomin hadin kan Nijeriya ne kuma bai kamata a yi wasa da su ba.
Nabena ya ce: “Idan har ingancin wadannan sassa a ka duba don mayar da su inda ya fi da cewa (Legas), mu ‘yan yankin Neja Delta muna rokon cewa, NNPCPL, NIMASA, NPA da sauran su za su fi da cewa a jihohin Bayelsa, Rivers ko Delta.
“Haka zalika ma’aikatar ma’adinai da karafa ta tarayya ta koma jihar Kogi inda muke da Babbar masana’anta ta Karfe da ke Ajaokuta.
“Na kuma yi imanin cewa, ko dai a mayar da ma’aikatar ciniki da zuba jari ta tarayya zuwa Kano ko kuma a mayar da ita jihar Anambra inda ake da manyan kasuwanni, haka ma a kai ma’aikatar noma ta tarayya jihar Binuwai, domin takenta shi ne ‘kwandon abinci na Kasa.”