Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanmu da kasancewa tare da wannan shafi me albarka. A wannan makon zan yi bayani wanda kacokan muka dauke shi daga kan rayuwar mu ta daidai muka mayar da shi rayuwar mu ta ba daidai ba, kuma shi ne ginshikin rayuwa ma’ana ilimi.
- Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Zan yi magana a kan ilimi musamman ilimin ‘ya’ya mata. Alal hakikanin gaskiya wani nazari da tunani muka yi muka gane cewar, “me ya sa yanzu muka fifita ilimin boko akan na addini, musamman ga ‘ya’ya mata?”.
Annabi ya ce mu nemi ilimi ko da a burnin Sin ne, sai dai wani abun tunani da hange a wannan yanayi da muke ciki, kowane iyaye burinsu da hangensu bai wuce na, Ya za a yi ‘ya’yansu su mallaki degree, babu ruwansu da la’akari cewar ya kamata ‘ya’yansu su san alkur’ani, su san Allah ba, wanda alkur’ani ilimin addini shi ne ilimin sanin Allah da manzonsa, kuma shi ne ilimin sanin addinin Allah.
Amma me ya sa hankalinmu ya fi karkata ga ilimin boko, za ka ga idan karatun boko za a kai yaro babu matsala, komai ake bukata za a yi, amma ilimin addini ba a bashi wannan gudunmawar.
Ita kanta gwamnatin da muke ciki za a ga rayuwar gwamnatin ta fi karkata da a taimakawa ilimin bokon, me ya sa muka yar da ilimin da Allah zai tambaye mu a kansa ranar gobe alkiyama?
Babu ruwan ubangiji da karatunka na boko, da aka ce ka je ka yi ilimi ba an ce ka je ka yi ilimin boko kadai ba, me ya sa muka fifita ilimin boko akan na addini?
Kowa ya fi ganin burgewa a kan ‘ya’yansa su iya turanci akan larabci, kullum idan ka yi magana sai a ce zamani ne ya zo da shi. Idan da za mu bawa kur’ani da addini mahimmanci fiye da ilimin boko wallahi tallahi akwai matsalolin da ba za mu shiga ba. Wannan mace-macen auren da suke yawa wallahi da ba su mutu ba, saboda wani lokacin a ilimin addini za ka samu mace ko namiji ya san ya ake aure, ya ake zaman aure, ya hakkin aure yake. Amma boko sai a ce ‘yan boko ne, da makamancin haka.
Ya kamata mu farga za a wayi gari lokacin da za a ga babu ma masu ilimin addinin da karfi ‘especially’ mata da ake yi wa aure, tunda burin kowa ne kawai ‘yar sa ta yi jami’a ta yi boko, ta samu ‘degree’, ta samu ‘masters’, ta zama abubuwa da yawa gashi nan dai. Sai ka ga rayuwar kawai tana tabarbarewa ana ta barin Allah, ana ta barin addinin Allah, ana ta barin hanyoyi na daidai, sai ace, ai ‘yan boko ne.
To, ni shawara nake bayarwa ba mu ce kar a yi karatun boko ba tunda zamani ne ya zo da shi, kuma shi ma ilimi ne. Amma ya zamanto iyaye da masu dama an yi fifti-fifti a bawa ilimin boko karfi, a bawa na addini karfi. Saboda rayuwar yanzu an tsinci kai cikin wata iriyar rayuwa ta gudun yada kanin wani akan tarbiyyar iyalai da ‘ya’ya da sauransu.
A da’ za ka ga makota ma suna iya tarbiyyar ‘ya’yan wani, amma yanzu mutum ma dakyar yake iya tarbiyyar nasa. Dan haka da ace tuntuni hanyoyin da muka bi na karatun boko haka muka bi na karatun addini, wallahi tallahi da tuni ilimin sani da tsoron Allah ya wadace mu sosai.
Allah ubangiji ya sa mu dace, Allah ubangiju ya amfanar da karatun da muka yi, ubangiji Allah ya kara buda kwakwalwar dalibanmu da mu kanmu bakidaya da sauran al’umma.












