Rahotanni sun nuna cewa sama da fursunoni 3,590 da aka yanke wa hukuncin kisa suna jiran a zartar musu hukunci ko a yi musu afuwa a gidajen yarin Nijeriya.
Adadin waɗannan fursunoni na ci gaba da ƙaruwa kowace rana, lamarin da ke haddasa matsanancin cunkoso a gidajen yarin ƙasar.
- Sallama Da 2024: Yadda Sin Ta Gudanar Da Diflomasiyya Ta Zaman Lafiya Ba Tayar Da Husuma Ba
- Ta Leko Ta Koma, An Cire Sunan Olmo Daga Jerin Yan Wasan Laliga
A shekarar 2022, hukumomin Nijeriya sun fara ɗaukar matakai domin rage wannan cunkoso.
A wancan lokaci, gidajen gyaran hali suna ɗauke da sama da mutane 74,000, duk da cewa doka ta ƙayyade iya karɓar mutane 58,278.
Hakan ne ya sa hukumomin fara tunanin yi wa wasu afuwa domin rage cunkoson.
Hukumomi dai sun fara kokarin rage cunkoson gidajen yari tun a shekarar 2022, amma har yanzu ana fuskantar ƙalubale, inda gidajen gyaran hali ke ɗaukar mutane fiye da adadin da aka ƙayyade musu.
Wannan na ƙara nuna buƙatar gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakan da suka dace wajen shawo kan matsalolin tsaro da kuma gyaran tsarin gidajen yari.