A ranar Juma’a, 25 ga watan Afrilun shekarar 2025 ce, aka daura auren Dauda Kahutu Rarara da amaryarsa Aisha Ahmad, wadda aka fi sani da Aisha Humaira, a birnin Maiduguri da ke Jihar Borno, an dade ana rade-radin akwai soyayya a tsakanin ma’auratan biyu, amma a duk lokacin da aka tambaye su, sai su ce; aiki ne ya hada su, ba wani abu daban ba.
A shekarar da ta gabata, Rarara ya rera wata waka mai taken ‘Aisha’, wadda a ciki ya baza kalaman soyayya; har aka yi ta cewa, da ita ya ke; amma sai aka yi amfani da wakar a wani fim da jarumar ta shirya mai suna, ‘A cikin biyu’, wanda Ali Nuhu ya hau a matsayin mijinta a wannan shiri.
- Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
- Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren, akwai jiga-jigan ‘yan siyasa, irin su tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin da sauransu, an daura auren kwana daya kacal da bayyana shirin auren da ma’auratan suka yi a shafukansu na sada zumunta.
Haka zalika, sun ki bayyana takamaiman wajen da za a daura auren, har sai bayan an kammala, inda suka bayyana yin hakan a matsayin wata hanya ta kawar da cece-kuce daga al’umma.
Kazalika a ‘yan watannin da suka gabata kuma, an sake daura auren jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau tare da angonta Ibrahim Garba, a wani biki wanda za a iya kira da na sirri da aka gudanar a birnin Kaduna, daura auren shahararriyar jarumar Kannywood din, Rahma Sadau da mijinta Ibrahim Garba, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya yi matukar bai wa mutane mamaki, duba da cewa; kafin daurin auren babu wata alama ko sanarwa da aka fitar daga makusantan mijin ko matar.
An yi bikin da safe, a Masallacin Atiku Auwal da ke Unguwar Rimi, inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka halarta, Rahma yayin da take magana da manema labarai ta bayyana cewa; ta zabi yin bikin cikin natsuwa ne, domin kauce wa hayaniya, bayan labarin ya bayyana a kafafen sada zumunta, ta tabbatar da daura auren nata.
Rahma ta shahara a fina-finan Kannywood da kuma wasu daga cikin fina-finan Nollywood, bayan da aka daura auren, masoyanta da abokan aikinta, suka tura mata sakwannin taya murna daga sassa daban-daban na Nijeriya, wannan aure ya zo ne watanni kadan bayan rasuwar mahaifinta, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Haka yasa ake saka alamar tambaya a kan jaruman masana’antar ta Kannywood, a kan cewa; me ya sa suke daura aurensu a sirrance? Yayin da wasu ke ganin yin hakan a matsayin wata hanya ce da jaruman ke bi wajen kauce wa bakin mutane, wasu kuma na ganin wannan a matsayin wata hanya ta nuna girman kai ko isa da jaruman ke bi, domin nuna wa duniya cewa; su ba kamar sauran al’umma ba ne.
Koma dai mene ne, akwai bukatar jaruman su tuna cewa; suna da dimbin mutane da ke kiran kansu a matsayin masoyan jaruman, wanda ko babu komai dai, bai dace a ce masoyinka ba shi da labarin wani abin alherin da ya same ka ba, musamman harka ta aure, wadda ka iya zama silar daina fitowa a fina-finai ga jarumai mata da mazajensu, ba su amince su ci gaba da harkar fim ba.