• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Karin Kamfanonin Ketare Suka Samu Ra’ayin Bai Daya Kan Zuwa Kasar Sin Don Raya Kansu?

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Bisa kididdigar da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fitar a kwanan nan, an ce yawan kudin jarin waje da kasar ta yi amfani da shi a watanni uku na farkon shekarar bana, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 408.45, adadin da ya karu da kaso 4.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, lamarin da ya shaida cigaban tattalin arzikin Sin ba tare da tangarda ba.

A cikin wannan adadi, yawan sabbin kamfanonin ketare ya zarce dubu 10, wanda ya karu da kaso 25.5 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara. Yadda kamfanoni ke shiga kasar Sin don kara samun bunkasuwa ya riga ya zama wani muhimmin batu da manyan kafofin watsa labarai na kasa da kasa suke tattaunawa a yanzu.

  • Tasirin Matsalolin Tsaro, Karancin Kudi Da Tsadar Rayuwa Ga Bukukuwan Sallar Bana

Akwai hasashen cewa, yawan kudin jarin da za a rika zuba wa sauran kasashe zai ci gaba da raguwa a shekarar 2023. Bisa wannan yanayin da ake ciki, kasar Sin ta sha wuya wajen samun wannan sakamako na jawon jarin waje, amma hakan ba abu ne da ya wuce zato ba.

Dalili kuwa shi ne, idan muka duba fannonin da kamfanonin suke zubawa jari, za a iya gano cewa, sun fi zuba wa kasar Sin jari ne a fannonin kimiyya da fasahohin zamani, da karin ingancin masana’antu, a kokarin more damammakin cigaban kasar Sin mai inganci.

A matsayin babbar kasuwa ta biyu ta sayen kayayyaki ta duniya, da babbar kasuwa ta farko ta sayar da kayayyaki ta yanar gizo ta duniya, babu shakka kasar Sin ta zama tamkar wani babban kek ga jarin waje. A waje daya kuma, kasar Sin da ke bude kofarta ga waje, na son more wannan kek na ta tare da sauran kasashen waje, tare da kara girmansa.

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kamfanin Tesla, da Airbus, da Astrazeneca, sun sanar da kafa masana’antu, da kara zuba jari a kasar Sin daya bayan daya, lamarin da ya shaida cewa, kamfanonin ketare na da kwarin gwiwa game da kasar Sin, domin sun gane cewa, zuba jari ga kasar Sin shi ne kokarin kago makoma mai haske.

Wasu rahotannin baya bayan nan sun bayyana cewa, ana sa ran shugaba Joe Biden na Amurka, zai sanya hannu kan wata dokar shugaba nan da wasu makwanni kadan masu zuwa, wadda za ta takaitawa kamfanonin Amurka adadin jarin da za su iya zubawa, a wasu muhimman fannonin tattalin arzikin kasar Sin, ciki har da fannin kirar bangarorin harhada na’urorin latironi na “semiconductors”, da fannin kwaikwayon tunanin bil adama na AI.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce ainihin dalilin Amurka na kakaba takunkumi a fannin jarin da ake iya zubawa a Sin, shi ne dakile ikon Sin din na samun ci gaba.

Wang ya kara da cewa, Sin na matukar adawa da wannan mataki, za ta kuma lura matuka da yanda abubuwa ke gudana, tare da daukar matakin kare hakkoki, da moriyar ta yadda ya kamata. (Kande Gao, Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Next Post
Sin A shirye Take Ta Tallafawa Ci Gaban Kasar Gambia

Sin A shirye Take Ta Tallafawa Ci Gaban Kasar Gambia

LABARAI MASU NASABA

Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

November 8, 2025
NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.