A tarihin mu’amalar da kasar Sin ta yi da kasashen yammacin duniya, rawar da Italiya ta taka na da halin musamman sosai. A tarihi, tsohuwar hanyar siliki ta hada wadannan tsoffin kasashe masu wayewar kai guda biyu. A cikin shekaru sama da 700 da suka wuce, matafiyi dan kasar Italiya, Marco Polo, ya yi tattaki zuwa kasar Sin, inda ya bude wa kasashen yammacin duniya tagar fahimtar kasar Sin, kuma labarinsa ya shahara a kasar ta Sin, har ma ya zama alamar abota ta kasashen biyu.
Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 20 da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Italiya. Kuma a kwanakin baya firaministar Italiya Giorgia Meloni ta yi ziyararta ta farko a kasar Sin a matsayin firaminista. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da ita a Beijing, inda bangarorin biyu suka ambaci “Ruhin Hanyar Siliki”.
- Sin Da Afrika Sun Himmatu Wajen Karfafa Hadin Gwiwar Dijital
- Me Ya Kawo Matasa Zuwa Yankin Xizang Na Kasar Sin?
To, ko me ya sa shugabannin kasashen biyu suka dora muhimmanci sosai kan “Ruhin Hanyar Siliki”? Wannan ba wai kawai saboda ya kasance tunanin tarihi, da kuma mahadar al’ummar Sin da Italiya a fannin al’adu ba ne, har ma ya dace da ra’ayoyin zaman lafiya, da bude ido, da hadin gwiwa da ke cikinsa, wadanda suka nuna halin musamman da aka kafa sakamakon mu’amalar da ake yi tsakanin Sin da Italiya, wanda ya dace da yanayin ci gaba kuma yana da daraja a zamanance.
Bisa ga “Ruhin Hanyar Siliki”, da yin amfani da hikimar tarihi, da kuma sanya sabbin abubuwa a sabon zamanin da muke ciki, hadin gwiwar kasar Sin da Italiya za ta kara zurfafa da kuma zama mai amfani, wadda za ta amfani kasashen Turai da ma duniya baki daya. (Bilkisu Xin)