Ba wannan lokacin bane ‘yan wasan kwallon kafa a duniya suka fara korafi a kan yawan wasannin da suke bugawa wanda hukumomin kwallon kafa na FIFA da EUFA suke kara musu a kan wadanda suke bugawa a baya.
Tun a shekarun baya tsohon kociyan Real Madrid da Manchester United, Jose Mourinho, ya yi korafi a kan yawan wasannin da ake sake karawa ‘yan wasa wanda hakan a cewarsa yana kawo gajiya ga ‘yan wasan kuma baya taimaka musu.
Tsohon kociyan Liberpool, Jugen Klopp, da na Manchester City, Pep Guardiola, sun yi korafi a kan yawan wasannin da hukumomi suke karawa wanda hakan yana kawo yawan jin ciwo da rashin kuzari ga ‘yan wasa.
A farkon wannan watan ne shima dan wasan Manchester City da kasar Belgium, Kebin de Bruyne, ya yi korafi a kan cewa suma mutane ne kamar kowa saboda haka wasannin da ake sake karawa sun yi yawa soasai.
Shima dan wasan Manchester City, Rodri ya ce ‘‘yan wasan na dab da yin yajin aiki, sakamakon da aka kara yawan wasannin da za suke bugawa wanda a cewarsa ya kamata a dinga tuntubarsu idan za a kara yawan wasanni saboda su ne suke bugawa.
Manchester City ta kara da Inter Milan ranar Laraba a Champions League, wanda aka kara wasa biyu kafin karawar zagaye na biyu a sabon fasalin babbar gasar Zakarun Turai ta bana wanda aka fara a ranar 17 ga wannan watan.
A gasar Club World Cup kuwa, inda Manchester City za ta fafata daga badi, an kara kungiyoyi sun kai 32, an samu karin wasanni da yawa kenan wanda hakan ne ya sa dan wasa Rodri ya ce yana jin suna dab da yin yajin aiki.
Ya ci gaba da cewa idan har an ci gaba da haka, za a kai lokacin da ba su da wani zabi sai dai kawai su tsunduma yajin aiki saboda suma mutane ne kamar kowa kuma suna da iyali kamar kowa amma za su dan kara jira su gani.
A sabon fasalin Champions League da Club World Cup na nufin Manchester City za ta buga karin wasanni hudu a kakar daga bana, fiye da yawan da ta fafata a bara wanda hakan zai kasance ‘yan wasa za su gaji sosai. Wasanni biyu kacal Manchester City ta yi ta kuma lashe Club World Cup a Disamba, amma a kakar badi za ta yi karawa uku a cikin rukuni da hudu a zagayen gaba har kai wa karawar karshe kuma a kakar wasa biyu baya,
Manchester City ta buga wasanni 120 a dukkan fafatawa, yayin da Rodri ya buga wasanni 63 a kwanaki 343 a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024.
Rodri, wanda ya buga wa tawagar Sifaniya da Manchester City wasa 63 a bara, ya lashe Premier League da kofin Nahiyar Turai da ya buga cikin wata biyu kuma bayan tashi daga Champions League karawar dab da karshe a gidan Real Madrid, Rodri ya sanar a cikin watan Afirilu cewar yana bukatar hutu.
Hakan ne ma ya sa bai buga wa Manchester City wasanni uku da fara kakar bana ba, ya fara daga 2-1 inda ta doke Brentford a Premier League ranar Asabar, kwana shida tsakani da ya yi wa Sifaniya Nations League.
Bayan kammala kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 wadda aka fara daga 6 ga watan Agustan shekarar 2023 da aka kammala a kwana 343, ranar 14 ga watan Yuli, Rodri ya sanar cewar yana bukatar dogon hutu fiye da wanda ake bashi.
Masana suna ganin yawan ciwon da wasu ‘yan wasan suke samu yana da alaka da yawan wasannin da suke bugawa domin ban da wasannin kungiyoyinsu, ‘yan wasan suna wakiltar kasashensu a wasannin gasa daban-daban ko kuma wasannin sada zumunta ko kuma na neman cancantar shiga gasa.