Kusan shekara guda kenan ake ta yamutsa gashin baki tsakanin wasu jiga-jigai biyu da ake ganin suna ta nunawa juna yatsu kan batun masarautar Kano, wanda a yanzu sarakuna biyu kowane ke kallon kawunansu a matsayin latattun sarakai, tsakanin sarkin na 15 da kuma 16 wanda guda ke cikin gidan Dabo, yayinda dayan kuma ke karamin gidan sarki na Nasarawa.
Idan dai za a iya tuna, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya kafa wani kwamitin da ya binciki zargin da suka yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda suka zarga da yi wa Gwamnatin Ganduje makarkashiya.
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
- Bana Cikin Wani Shiri Na Tsige Sanusi II A Matsayin Sarkin Kano – Ganduje
Bayan faduwar gwamnatin da ake ganin ita ce ta yi sanadiyyar tsige Sarki Muhammadu Sanusi, sai gwamnatin NNPP wadda ke adawa da matakan da aka dauka kan sarki Sanusi ta samu nasarar daman daukar matakin mayar da shi, wanda daman hakan na cikin alkawarin da Kwankwasiyya ta yi, saboda haka ba a dauki lokaci ba sai aka gabatar da bukatar sake duba dokar da majalisar dokokin lokacin Ganduje ta zartar wadda aka yi amfani da ita wajen cire Sanusi II.
Bayan shigar da Muhammadu Sanusi II gidan Dabo cikin dare, sai Sarki Aminu ya dawo daga tafiyarsa washegari inda ya wuce karamar fadar da ke gidan Sarki na Nasarawa, wanda tun daga wancan lokacin a karon farko sarakuna biyu ke gabatar da mulkin masarautar ta Kano daga wurare daban-daban.
Babban kalubalen da Sarkin Sanusi ke fuskanta shi ne, rashin samun goyon bayan gwamnatin tarayya, musamman ganin jam’iyyar APC ke mulki, wanda shi kuma Sarki Sanusi jama’a sun gamsu da yadda ya taimaka wajen kayar da jam’iyyar a Kano, saboda alkawarin da Kwankwasawa suka yi masa na dawo da shi kan kargar sarautar Kano.
Sarki Aminu wanda ke samun goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma umarnin wasu kotuna guda biyu da hukuncinsu ya tabbatar da shi a matsayin halastaccen sarki, ya kasance yana ci gaba da aiwatar da harkokin mulki daga waccan karamar fadar, tare da fuskantar kalubale daga bangaren Gwamnatin Jihar Kano, wadda har majalisa aka kai bukatar rushe katangar gidan sarkin na Nasarawa da sunan za a gyara gidan.
Sakamakon wannan ne ya sa tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa ake ganin yana cikin wadanda suka hana Sarki Sanusi II rawar gaban hantsi, sannan kuma ya toshe duk wata kofa da gwamnatin Kano ka iya samu wajen karfafa mulkin Sarkin Sanusi, sannan akwai kotuna guda biyu duk na gwamnatin tarayya ne wadada hukuncinsu ya bai wa Sarki Aminu gaskiya a shari’un da ke gabansu, saboda haka hukuncin da ake sauraro yanzu shi ne ka iya nuna makomar Sarki Sanusi II da kuma shi kansa Sarki Aminu.
Sai dai kuma daga irin abubuwan da ake gani a duk lokacin da wani daga cikin sarakunan biyu ya fito cikin al’umma, ana iya fahimtar wanda talakawa suka fi sha’awa, musamman duba da dawowar Sarki Sanusi daga kasar Ingila, lokacin ya je kare digirin-digirgir dinsa, yayin da shi kuma sarki Aminu ya halarci taro da aka saba gudanarwa duk shekara a masallachi Marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u.
Saboda haka batun da ake na cewa Dakta Ganduje na shirya wata kulalliya domin tabbatar da sallamar Sarki Sanusi II ba wani sabon abu ba ne, domin yana daga cikin alkawuran da gwamnatin Kano ta yanzu ke kansu na yin duk mai yiwuwa wajen rushe duk wani tsari na Ganduje, sannan kuma kusancinsa da shugaban kasa, musamman kasancewarsa shugaban jam’iyyar da Bola Tinubu ya ci zabe karkashin tutarta.
Muhimmancin Jihar Kano a wurin gwamnatin tarayya ya sa wasu ke ganin su Ganduje za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun hana Sarki Sanusi zama a karaga.
Yanzu haka akwai kishin-kishin cewa, Ganduje ya tattaro mukarabbansa ciki har da ‘yan kasuwa da manyan dattawan jihar domin neman Shugaba Bola Tinubu ya sa baki Sarki Sanusi da Sarki Aminu kowa ya hakura domin samun maslaha.
Sai dai har yanzu abin na nan lullube a cikin duhu wanda lokaci ne kadai iya tabbatarwa.