• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Zai Biyo Bayan Canza Wasu Kudade A Nijeriya?

by Leadership Hausa
3 years ago
Kudade

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce za su yi hakan ne bisa bukatar gwamnatin tarayya da kuma amincewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda matakin, zai shafi takardar naira 200 da naira 500 da kuma naira 1000.

Bankin ya ce za a yi wannan sauyi ne domin rage yawan kudin da ke yawo a hannun jama’a da rage hauhawar farashi da kuma magance yin jabunsu.

  • Sin Ta Sanar Da Shirin Bunkasa Fasahar VR
  • Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin PDP A Kaduna Ta Tsakiya, Ta Bada Mako 2 A Sake Wani Zaben

A dangane da hakan ne bankin ya bukaci masu kudi a hannu su mayar da su bankuna cikin kasa da kwana 50.

Haka kuma CBN, ya ce sabbin kudaden da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022.

Ya kara bayani da cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2023.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

A shekarar 2014 Babban Bankin ya sauya takardar naira 100 domin murnar cikar Nijeriyar shekara dari daya da Turawan mulkin mallaka suka hade Kudanci da Arewacin Kasar a 1914.

Sai dai wannan shiri na canza fasalin kudin, ya haifar da cece-kuce mai zafi a kasar. Wasu kuma suna ta tambayar, meye zai faru bayan wa’adin da babban bankin ya bayar ya kare?

Bayan wa’adin da bankin ya sa na 31 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2023, mutane ba za su iya amfani da tsofaffin takardun kudaden ba kuma.

A bayanan da bankin ya bayar ya ce, dukkanin bankunan da ke da wadannan takardun kudi a yanzu suna iya fara mayar da su CBN ba tare da bata wani lokaci ba.

Gwamnan bankin ya ce, duk bankin da ya fara kaiwa shi za a fara bai wa sabbin takardun.

Ya shawarci jama’a masu mu’amula da bankuna wadanda suke da kudaden a hannunsu da su fara kaiwa asusun ajiyarsu a bankunan domin a samu damar sauya su da wuri.

A sakamakon matakin ana sa ran dukkanin bankuna su bar cibiyoyinsu na tattara kudade a bude daga Litinin zuwa Asabar, saboda wannan shi ne zai bayar da dama ga jama’a su mayar da kudaden a kan lokaci.

Domin hanzarta sauyin, Babban Bankin na Nijeriya ya dakatar da cajin kudin da ake biya na ajiye kudade a bankuna.

Amma kuma sanarwar ta ce idan yawan kudin ya wuce N150,000 za a biya caji.

Da aka fara samun soke-soke da cewa babban bankin kasar bai bi ka’ida ba wajen yin canjin kudin a daidai wannan lokaci, sai

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, ya bi doka da ka’ida wajen sauya fasalin takardun kudin kasar uku da yake shirin yi.

Kakakin CBN, Mista Osita Nwanisobi, na mayar da martani ne ga Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmed, wadda ta ce ba a tuntubi ma’aikatarta ba kafin aiwatar da sauyin.

Da take magana lokacin da ta bayyana a gaban wani kwamatin Majasliar Dattawa ranar Juma’a da ta gabata, Zainab ta soki shirin tana mai cewa “ba lokacin da ya dace ba ne”.

Sai dai Mista Nwanisobi ya ce hukumomin CBN sun bi ka’ida wajen neman amincewar Shugaba Buhari kamar yadda sashe na 2(b) da sashe na 18(a) da sashe na 19(a) (b) na dokar CBN ta 2007 suka tanada don neman sauya fasali da samarwa da fara aiki da kuma yada sabbin takardun kudi na N200 da N500 da N1,000.

A ranar Laraba ne babban bankin ya ba da sanarwar sake takardun na naira, inda ya ce kashi 80 cikin 100 na kudaden kasar na hannun mutane maimakon bankunan kasuwanci.

CBN ya bai wa ‘yan kasar wa’adin kwana 47 da su mayar da kudaden ga bankunan kasuwanci kuma yana sa ran nan da 15 ga watan Disamba mai zuwa zai fitar da sabbin takardun N200 da N500 da N1,000.

Tarihin Kudin Nijeriya

A shekarar 1880: Kudin farko na Nijeriya shi ne na Shillings (Sulai) da Pence (Kwabo). Tsabar kudin wanda Babban Bankin Ingila ya samar shi ne na

Sulai daya ( Kwabo 12) da 1 Penny wato Kwabo 1 da kuma 1/10, kuma bankin ‘yan kasuwa mai suna Bank for British West Africa shi ne yake rarraba kudin har zuwa shekarar 1912.

Daga shekarar 1912 zuwa 1959: Hukumar samar da kudade ta Afirka ta Yamma (West African Currency Board (WACB), ta samar da takardun kudi da tsaba na farko ga kasashen Nijeriya da Ghana da Saliyo da kuma Gambia. Kuma babbar takardar kudi ta farko ita ce, ta fan daya, yayin da sulai daya shi ne tsabar farko babba a lokacin.

A shekarar 1959: Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya samar da takardun kudin kasar na farko, yayin da kasar ta daina amfani da takardar kudi da tsabar da bankin kasuwancin na hadakar Afirka ta Yamma WACB yake samarwa.

A shekarar 1962: A wannan shekarar ne aka sauya yanayin kudin na Nijeriya, ya nuna matsayinta na mai cin gashin kanta sabanin a baya, lokacin da take karkashin mulkin Turawan Birtaniya. An sauya Kudin da ke dauke da rubutun ’FEDERATION OF NIGERIA‘, zuwa wanda aka rubuta ‘FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA’, a sama.

A 1968: A wannan shekarar aka sake sauya takardar kudin saboda yadda aka saba amfani da su a lokacin yakin basasa.

A 1973: An sauya sunan kudin Nijeriya daga fan 1. An bullo da naira daya wadda take daidai da sulai goma a matsayin babbar takardar kudin kasar. Yayin da kananan kudin da ake kira kwabo (kobo) guda dari ya zama naira daya.

A 1977: A wannan shekara aka bullo da sabuwar takardar kudi ta naira Ashirin (N20). A lokacin ta kasance takardar kudi mafi girma a kasar wadda Babban Bankin ya bullo da ita saboda bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma bai wa jama’a damar walwalar rike kudade masu yawa ‘yan kadan maimakon tilin takarda. A karon farko an sa hoton wani fitaccen dan kasar a kan takardar kudin.

A shekarar 1979: An bullo da sabbin takardun kudi uku, na naira daya da naira biyar da kuma naira goma (N1, N5, N10). Domin mutane su iya ganewa tare da bambanta takardun an yi masu launi iri daban-daban. Sannan a bayan kowace takarda aka sanya hoton wasu abubuwa da ke nuna al’adun kasar.

A 1984: An sauya dukkanin launin takardun kudin in banda takardar kobo 50 a cewar hukuma domin shawo kan yadda ake ficewa da kudin kasar waje a lokacin.

A shekarar 1991: An sauya takardar kobo 50 da naira daya zuwa tsaba.

A shekarar 1999: Domin abin da hukuma ta ce fadada harkokin tattalin arzikin kasar da saukaka cinikayya, aka bullo da takardun kudi na naira dari daya da naira dari biyu da naira dari biyar da kuma dubu daya ( N100, N200, N500 da N1000) a watan Disamba na 1999 da Nuwamban 2000 da Afrilun 2001 da kuma Oktoban 2005.

A shekarar 2007: A matsayin wani bangare da sauye-sauyen tattalin arziki an bullo da takardar kudi ta naira Ashirin ta leda a karon farko. Yayin da kuma aka sauya fasalin zanen naira hamsin da naira goma da naira biyar har da naira daya da kuma kobo hamsin, sannan aka bullo da tsaba ta kobo biyu.

A shekarar 2009:  Sakamakon irin amfanin da gwamnati ta ce ta gani dangane da sauya takardar kudin naira Ashirin zuwa ta leda, sai ta sauya naira hamsin da goma da kuma naira biyar zuwa na leda. A yanzu dukkanin kananan takardun kudin kasar na leda ne.

A shekarar 2010 da 2014: babban bankin kasar CBN, ya bullo da sabuwar takardar naira hamsin da ta naira dari domin bikin cikar Nijeriya shekara 50 da samun ‘yancin kai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
2023: Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC A Kaduna

2023: Kotu Ta Tabbatar Da Uba Sani A Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

October 21, 2025
NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.