Daga Bashir Abusabe
Kamar yadda muka sani a rayuwar adabin Hausa ya biyo zanguna mabambanta, wannan ba sai an yi dogon sharhi ba, domin kuwa daga tashin Hausawa na zaman gargajiya har zuwa lokacin da suka cudanya da baki an sami sauye-sauye da adabin Hausawa ya yi ko dai ta fuskar sauyawar riga daga ta gargajiya zuwa ta zamani (Larabci ko Ingilishi ko Faransanci) ko kuma ta sauyawar kayan cikin adabin saboda haduwa da sababbin ladubban rayuwa . Irin sauye-sauyen da aka samu daga gargajiya zuwa zamani abu ne da masana sun sha ambatonsa, kila abin da ba a fi mayar da hankali kai sosai ba shi ne yadda gwamutsuwa da bakin al’amurra ke haifar da sababbin batutuwa da ke bukatar kara bincike da nazari.
Batutuwan da suka yi tashe a cikin ‘yan shekarun nan, musamman abin da ya shafi kagaggun labaran Hausa, bai wuce batun nan na Adabin Kasuwar Kano ba, wato littattafan da yawancinmu ke kira Labaran Soyayya da suka tuzgo daga sassa daban-daban na kasar Hausa da ke hedikwata a birnin Kano. Samuwa da watsuwa ko kuma karbuwa da kuma ce-ce-ku-ce da wannan sabon salon adabi ya samu kansa a ciki, tsakanin marubuta da manazarta da masana a kasar Hausa da ma sassan duniya daban-daban ya jawo ayyukan nazari da musayar miyau mai tarin yawa.
Abin da za mu yi kokarin yi a nan shi ne shimfida tabarmar nazari game da wannan fage ta hanyar neman sanin yadda adabin kasuwa yake ta hanyar tambayar ko akwai wani abu wai shi adabin kasuwa? Idan akwai shi to a yaya yake? Shin ana iya samunsa a kasashe masu tasowa kamar Nijeriya? Ko kuwa dai wanda ake da shi da ake kira Adabin Kasuwar Kano, an sa masa sunan ne domin cin mutunci da batunci ko son rai?
Idan kuma ka dauki ma’anar Adabin Kasuwa a luggance da ke nufin adabi na kowa da kowa ko na yayi ko abin da ke jan hankalin jama’a a kodayaushe, ke nan ana iya cewa akwai adabin da ke da akasin haka, ma’ana adabin da ba na kowa da kowa ba, adabin manya, masu ilmi ko sarauta ko daraja a tsakanin al’umma, a takaice dai adabin da ke shimfide a wani wuri domin manazarta da masana ko kuma wanda fagensa ba na kowane dan tagaja-tagaja ba ne wajen saye da karantawa da nazari, wato abin da ake wa lakabi da gangariyar adabi.
Saboda haka kokarinmu a nan shi ne mu bambanta tsakanin gangariyar adabin da wanda ake wa lakabi da na kasuwa, domin ta haka ne za a gane yadda tunanin samuwar Adabin Kasuwar Kano ya tusgo, yake kuma gudana. Adabi dai kamar yadda masana suka yi nuni, kundi ko hoto ko madubi ne, (dubi Dangambo, 1984, da Gusau, 1995 da Malumfashi, 2002) da ke d dauke ko nuna hanyar gudanar da rayuwar al`umma. Za a iya fahimtar irin wannan adabi ta yin la`akari da abubuwa guda biyu; Na farko shi ne harshen da ake amfani da shi, wanda yake makunshin tarihi, kuma linzamin bayyana tunani ko kuma wata manufa.
Na biyu kuma ita ce fasaha, wadda ita ke bayyana tunanin da ke cikin zuciya a aikace, kamar yadda Muhammad, (2001) ya bayyana. Shi kuma Cuddon,(1999) da yake kokarin fitar da ma’anar adabi a luggance, cewa ya yi adabi na iya kasancewa abubuwa da dama da suka hada da wasan kwaikwayo da waka da gajerun labarai da rubutattun litattafai da dai sauransu. Ya ci gaba da cewa idan har aka ce wannan aikin adabi ne, to makunshiyar aikin ta bambanta da sauran kwashe-kwashe na yau da kullum, musamman idan abin ya shafi gaskiyar lamari ko kuma fadar tarihi, ke nan adabi yana da wasu siffofi da suka bambanta shi da wasu ayyuka da ba su da tasiri irin nasa.
Duk da haka akwai ayyuka ko rubuce-rubuce da dama wadanda ba a yi su don su kasance na adabi ba ne, amma kuma za a iya sanya su cikin aikin adabi; saboda ingancin aikin da asalinsa ko kuma irin kyaau da kuma fasahar da aka nuna wurin rubuta shi, kamar yadda (Cuddon, 1999) ya nuna. Daga wannan hasashe za a iya cewa, adabin da ke da wadannan siffofi da aka ambata a sama, shi ne ke kasancewa gangariyar adabi, akasin haka kuma sai ya zama wani abin, kila ma na kasuwa ko kuma gwanjo ko makamancin haka.
Kamar yadda kowane sashe na duniya yake da gangariyar adabi, to haka a wasu sassan duniya ake da adabin kasuwa, (Market Literature) ko kuma adabin yayi (Popular Literature). To amma idan muka ce adabin kasuwa, nan zai iya kasancewa na yayi, domin kuwa duk abu daya suke tattaunawa. Duk abin da ya kasance na kasuwa to yana da alaka da yayi. Kasuwa dai wuri ne da ake saye da sayarwa na dukkan abubuwan rayuwa, duk wanda ke cikin wannan al`umma yana iya zuwa cikinta domin yin kasuwancinsa.
Saboda haka adabin kasuwa wani bangare ne na adabin al’umma da kowa zai iya shiga cikin kogin ya yi iyo ko kurme; masani ko malami ko manazarci ko akasin haka. Ke nan irin wannan adabi wani abu ne ko dai waka ko wasan kwaikwayo ko kananan labarai, ko rubutattaun litattafai da aka tsara a wani zangon rayuwar jama’a, ake kuma tsintar su a tsakanin jama’ar ba tare da wani kandagarki ba.
Ta fuskar sayar da su ba a yi wani tanadi na wurin da ya dace ba, ko dai a same su a kasuwa ko wurin hirar matasa ko tsakanin matan aure ko makarantu ko kuma ma duk inda jama’a ke tururuwa domin karatu da rubutu. Haka kuma idan aka ce adabi na yayi ne ana nufin cewa zai rayu daga wani lokaci zuwa wani, wato akwai lokacin da yake tashe, akwai kuma lokacin da yake sallacewa, sai a bar masana da yin rubdugu kansa, (Malumfashi, 2002).
Kai ba wannan ba ai masana da dama ba su dauki aikin adabi irin wannan abin tokabo ba, shi ya sa ba a damu da sanin inda ya sa gaba ba. Sai dai ko da aka soma nazarin nasa daga baya, an kuma shigo da ayyukan adabi da mutum na iya cewa ba irin na adabin kasuwa ko yayin da aka saba ji da gani ba ne.
A halin yanzu daga cikin ayyukan adabin kasuwa ko na yayi da ake da su an sanya irin kagaggun labaran da a da ba su cikin irin wannan rukuni, wato irin wadanda suka hada da labaran bincike ko tsafi ko na ban tsoro ko soyayya ko na Amurkawan dauri ko na ban dariya ko kimiyya, wato dai kagaggun labarai da milyoyin jama’a ke saye da karantawa a sassan duniya daban-daban ko da kuma ba a nazarin su a ajin adabi ko jami’o’i, musamman daga shekarun 1930. Har yau takaddama ba ta kare ba dangane ko wadannan irin ayyukan adabi na gangariyar adabi ne ko kuma kwamacala.
Ga masana kamar yadda aka bayyana a (eNotes.com ), irin wannan aikin adabi na kasuwa bai da nasaba da aikin kwarai, ana nuni da cewa dabara ce kurum ta samun kudi da suna, amma ba adabin da za a ta da jijiya wajen karatu ko nazari ba ne. Fasalin Adabin Kasuwa A Duniya Daga nazarin da aka gudanar an fahimci cewa adabin kasuwa ko na yayi yana tafiya ne kafada da kafada da gangariyar adabin al’umma. Shi gangariyar adabin yana kasancewa ne tsakanin masu ilmi ko hannu da shuni ko kuma iyayen kasa.
Duk wani abu da ba na wannan gungun mutane ba, yawanci shi ake wa lakabi da adabin kasuwa ko yayi. Alal misali kusan duk yawancin ayyukan adabi da suke da wannan siffa a Turai ko Amurka ko sauran sassan duniya an samar da su ne tsakanin karni na 16 da 17 da na 18, daidai lokacin da fasahar dab’i ko buga littattafai ta yi tashe a duniya. Kamar yadda bayanai suka yi nuni, yawancin jama’a da masana idan ana maganar adabin karni na 16 da 17 da na 18, ana maganar gangariyar adabi ne ko na masu ilmi ko mulki ko dukiya, amma ba su kadai ne suka kwashi nasu kason ba daga rayuwar adabi, akwai adabin talakawa ko na kasuwa, wato na kowa da kowa. Ma’ana, an samar da adabin da aljihun talaka zai iya biya, ya saya don karantawa.
Wannan dama ta samu ne domin an samar da injinun buga littattafai na bakin hanya da suka ba talaka damar ya sami gurbin da zai buga nasa adabin. Ire-iren wadannan ayyukan adabin su ne ake ba sunaye daban-daban da suka hada da Grub Street Literature ko Chapbooks. Wadannan lakabobi sun wanzu ne saboda la’akari da irin yadda aka samar da adabin ko wuraren da ake samar da littattafan ko kuma yanayin buga da sayar da su.
Su dai Grub Street Literature su ne ayyukan adabin da aka samar daga wuraren buga littattafai da ke kan Titin Grub a Landon. Da yake a tsakanin karni na 16 da 17 da na 18 an samar da marubuta na kwarai, sai dai rubutun nasu ya fi mayar da hankali ne ga masu-fada-a-ji, bai ta’allaka ga sauran jama’a ba, ga shi kuma sun fi sauran jama’ar yawa, wannan ya sa aka shiga neman wasu da za su agaza da nasu rubutun.
Sai dai yawancin irin wadannan marubuta ba su da sanayya ta zamani game da fasahar rubutu da kaga labarai, shi ya sa idan sun yi rubutu ake biyan su kudade kadan, wannan ya sa suke rayuwa a cikin talauci da kunci. Shi kansa inda suke zama a bakin titin domin yin aikin nasu na adabi, wuri ne na kazanta da yawan lalata da tashin hankali; nan ake samun barayi da mabarata da dai ire-irensu; nan ne marubutan da injinan buga ayyukansu suka daura aure. Su kuwa Chapbooks littattafai ne da ake wa lakabin littattafai masu arha, su ne ayyukan adabin da suka kasance na yayi ko na jama’a a karo na farko a wancan zamani na karni na 17 da 18.
Ba ruwansu da kamfanonin hukuma ko na gwamnati, ba kuma ruwansu da manyan kamfanonin dab’i da ke neman kazamar riba. Ana kuma shirya da buga irin wadannan littattafai domin isar da sako ga talakawa ko masu sha’awar adabi, amma ba su da kudin sayen gangariyar adabin da ke wanzuwa a lokacin. Wannan damar ce marubutan da masu karatu ke amfani da ita domin su isar da sako ga sauran jama’a ba tare da kamfanin dab’i ya sa baki ba, yawancin abubuwan da ake samarwa sun hada da wake-wake da labarai da ayyukan addini da sakonnin siyasa da makamantansu.