Ranar 12 ga watan Janairu na shekarar 2024 da muke ciki shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya nada shahararren jarumin fina finan Kannywood Ali Nuhu matsayin shugaban hukumar shirya fina finai ta Nijeriya (Nigeria Film Cooperation).
Hakan ya sa LEADERSHIP Hausa ta yi dogon bincike domin bayyanawa masu karatu ainahin aikin wannan hukuma.
- Ina Rubutu A Kan Rayuwar Yau Da Kullum Domin Mutane Su Wa’azantu – Fatima Sunusi
-  ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Da Ake Zargi Da Satar Mutane A Abuja
Nigeria Film Corporation hukuma ce mallakin gwamnati da ke sarrafa fina-finan Nijeriya wadda aka kafa ta a cikin shekarar 1979 a karkashin doka mai lamba 61 na kundin tsarin mulkin Nijeriya 1979.
Hukumar ta NFC a takaice tana aiki ne a matsayin cibiyar gwamnatin tarayya wacce aka dorawa duk wani alhaki na ganin masana’antar fina finan Nijeriya ta tsayu da kafafunta kuma ta fitar da kyawawan halaye da al’adun yan Nijeriya a idon duniya.
Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu ta Tarayya ke kula da ita kuma ta bata duk wani iko da take bukata domin bunkasa al’adu ta hanyar sinima a Nijeriya.
Ta hanyar ayyukanta hukumar tana bayarda gudummawa sosai ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.
Samar da fina-finai don amfanin gida da fitar da su zuwa kasashen waje na daga cikin muhimman aiyuka da wannan hukuma take gudanarwa.
Wasu daga cikin aiyukan wannan hukuma shine samarwa da kuma kula da kayan aikin shirya fina-finai,karfafa gwiwar shirya fina-finai da ‘yan Nijeriya ke yi ta hanyar kudi da sauran nau’o’in taimako,samar da wuraren horarwa da adana fina-finai, kayan sauti da na bidiyo da sauransu.
Saye tareda rarraba fina-finai ga wuraren da suka kamata,tallafawa masana’antun shirya fina finai,shirya bukukuwan baje kolin fina finai da fasaha na cikin gida Nijeriya da kuma na kasa da kasa,gudanar da bincike kan abubuwan da suka shafi fim da masana’antu baki daya.
Wadannan sune muhimman ayyuka da wannan hukuma da aka baiwa jarumi Ali Nuhu shugabanci take gudanarwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp