Daga Abba Ibrahim Wada
Kungiyoyin Manchester City da Paris St-Germain sun samu dama domin Messi, daya daga cikin manyan ‘yan kwallon kafa na duniya ba shi da kungiya bayan karewar kwantiraginsa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
Haka ne, domin kuwa wata 12 bayan ya yi yunkurin da ya hana shi barin Barcelona, yanzu dai Lionel Messi ba shi da kwangila a kungiyar domi kwangilar dan wasan na Argentina ta kare ne da tsakar daren ranar Alhamis kuma duk da jita-jitar da aka kwashe wata da watanni ana yi, bai sabunta zamansa a kungiyar ba.
An yi amannar cewa ana tattaunawa kan sabunta kwangilarsa, ma’ana dai Messi yana iya yanke shawarar zama a Nou Camp amma dai a halin yanzu, yana zaman kansa ne ba tare da wata kungiya ba.
Wacce kungiya Messi zai tafi a kakar wasa mai zuwa?
A farkon makon nan marubuci kan harkokin wasanni a Sifaniya Guillem Balague ya ce Barcelona tana matsa lamba kan dan wasan domin ganin ya sabunta kwangilarsa kafin a shiga watan Yuli.
“Sabunta kwangilar Messi ita ce babban abinda shugaban kungiyar Joan Laporta ya saka a gaba kuma a halin yanzu yana tattaunawa kai tsaye da mahaifin dan wasan Jorge Mess da wakilinsa,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa ” Idan kungiyar tana so ta rike dan kasar ta Argentina, dole ne ta rage alawus-alawus dinsa da kimanin euro miliyan 200 (£172m) domin ta cika ka’idar hukumar La Liga.
Messi yana sane cewa wasu kungiyoyi suna son daukarsa, sai dai har yanzu bai yi takamaimiyar magana da su ba, domin kuwa yana so da farko ya ga kwangilar da Barcelona za ta ba shi.
Ana alakanta dan wasan mai shekara 34 da son tafiya daya daga cikin kungiyoyin Paris St-Germain ko kuma Manchester City, inda zai hadu da tsohon kocinsa a Barcelona Pep Guardiola sai dai a halin yanzu yana can Brazil inda yake buga wa Argentina wasa a gasar Copa America.
Yunkurin da Lionel Messi ya yi na barin Barcelona.
A ranar 25 ga watan Agustan 2020 – Messi ya aike wa kungiyar sako yana mai cewa yana son barinta nan take.
4 ga watan Satumban 2020 – Messi ya ce zai ci gaba da zama a Barcelona saboda babu wata kungiya da za ta iya biyan yuro miliyan 700 (£624m) a matsayin kudin darajarsa kafin ya bar Barcelona sannan a ranar 27 ga watan Oktoban 2020 – Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu, wanda yake zaman doya da manja da Messi, ya sauka daga mukaminsa.
28 ga watan Disambar 2020 – Messi ya ce yana fatan watarana ya buga wasa a Amurka, ko da yake ba shi da tabbas kan makomarsa idan kwangilarsa ta kare a Barcelona haka kuma a 31 ga watan Janairun 2021 Barcelona ta ce za ta dauki matakin shari’a da ya dace a kan wata jaridar Sifaniya El Mundo bayan ta wallafa kwangilar Messi ta shekaru hudu wadda ta kai £492m.
16 ga watan Mayun 2021 – Kocin Ronald Koeman ya ce yana fatan Messi ba wasansa na karshe ya yi wa Barcelona ba bayan sun sha kashi da ci 2-1 a hannun 2-1 defeat by Celta bigo lamarin da ya dusashe fatansu na daukar kofi abin da ke nufin ba sa cikin kungiyoyi biyun farko a karon farko tu kakar 2007 zuwa 2008.
22 ga watan Mayun 2021 an yi amannar cewa Paris St-Germain ta kusa kammala daukar Messi har ila yau a ranar 28 ga watan Mayun shekara ta 2021 shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce har yanzu ba a cimma matsaya kan sabunta kwangilar Lionel Messi ba amma dai komai yana tafiya daidai.
1 ga watan Yulin 2021 – Kwangilar Messi a Barcelona ta kare kuma ya zama dan wasa mai zaman kansa.