Dan wasan tawagar Argentina Lionel Messi, ya kamo tarihin da tsohon dan wasan Brazil, Pele, ya kafa na cin kwallaye 643 a kungiya daya, bayan kwallon da ya ci wa kungiyarsa ta Barcelona a wasan da ta buga da Balencia ranar Asabar.
Messi ya buga wa Barcelona da ke Sifaniya wasanni a kaka 17 da ya yi, tun bayan fara wasansa a shekarar 2004 kuma gwarzon dan wasan Brazil ya fi kowa yawan cin kwallaye a kungiyar Santos a kakanni 19 da ya buga da kungiyar.
Har ila yau Messi na cikin manyan ‘yan wasan duniya da suke haskakawa sama da shekara 10 a jere, tare da takwaransa na Juventus Cristiano Ronaldo wadanda cikin shekaru goma na baya suka mamaye kwallon kwafa ta hanyar lashe kowacce irin kyauta ta nuna bajinta.
Sai dai a wannan kakar Messi na fuskantar koma baya na rashin kokarin kungiyarsa ta Barcelona wadanda wasu ke dora alhakin hakan a kan shi duk da cewa a kwanakin baya ya bayyana cewa yana son barin kungiyar
Sharadin kuwa shi ne dole duk kungiyar da ke son sayensa ta biya yuro miliyan 700 kudin darajar dan wasan kuma mafi yawan kungiyoyi sun ce ba za su iya cika sharadin ba lamarin da ya sa Messi ya fasa barin kungiyar a watan Agustan da ya wuce.