Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jajanta wa iyalan Hajiya Rafat Salami, babbar ‘yar jarida a gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) kuma Ma’ajin Cibiyar Yaɗa Labarai ta Duniya (IPI), wadda ta rasu a ranar Juma’a a Abuja.
Da yake bayyana rasuwar tata a matsayin “babban rashi ba kawai ga iyalan ta ba, har ma ga harkar aikin jarida ta Nijeriya,” ministan ya yaba wa sadaukarwar ta ga aikin jarida.
- Babban Aikin “Samar Da Lantarki Daga Hasken Rana A Wajen Da Ake Kiwon Kifi” A Sin Ya Fara Aiki
- Kudirin Dokar Haramta Amfani Da Kudaden Waje Ya Tsallake Karatu Na Farko A Majalisa
Ya jaddada cewa ta shafe shekaru 23 tana aiki a gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), inda ta kai matsayin Daraktar Sashen Watsa Labarai na Zamani, tana horar da matasa masu zuwa cikin masana’antar.
A cikin saƙon ta’aziyyar sa, Idris ya ce, “Rasuwar ta ta bar babban giɓi a cikin ma’aikatan VON da kuma a IPI reshen Nijeriya, inda ta sadaukar da kan ta wajen kare haƙƙin ‘yan jarida, inganta ‘yancin yaɗa labarai, da tabbatar da jin daɗin ‘yan jarida, kuma kwanan nan aka sake zaɓen ta a matsayin ma’aji.”
Ya ƙara da cewa, “Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalan ta da ma’aikatan VON, da IPI Nijeriya, da dukkan masana’antar aikin jarida a Nijeriya bisa rashin irin wannan fitacciyar mace. Allah ya jiƙan ta da rahama kuma ya bai wa iyalan ta ƙarfin jure wannan rashi.”
A nasa saƙon ta’aziyyar, Darakta Janar na VON, Malam Jibrin Baba Ndace, ya bayyana Salami a matsayin “abar misali na ƙarfi, tausayi, da ƙwazo.”
Ya ce rasuwar ta ta bar dukkan iyalan VON cikin tsananin baƙin ciki.
Ya ce: “Misis Salami ba kawai ƙwararriya ba ce; ta kasance misali na ƙwarewa, gaskiya, da sadaukarwa.”
Ndace ya ƙara da cewa, “Gudunmawar ta ta ban-mamaki ga aikin jarida da rawar da ta taka wajen cigaban kafofin sadarwa na zamani a VON sun kasance abin a yaba.
“An san ta da aiki tuƙuru, iya yare da dama, da kuma jajircewa ga nagarta, ta kasance misali na ƙwarewa da ƙwazo.
“Dangantaka ta da Hajiya Salami ta fara ne kafin in zama Darakta Janar na VON. Bayan naɗin da aka yi mini, ko yaushe nakan nemi shawarwarin ta masu matuƙar muhimmanci kuma nakan dogara da goyon bayan ta wajen ƙoƙarin mu na gyara hukumar.”
Ndace ya bayyana cewa duk da matsalolin lafiyar ta, Salami ta taka rawar gani a wani taron da VON ta gudanar a baya-bayan nan.
Ya ce: “Na kira ta a lokacin taron don yi mata addu’ar samun lafiya, ban taɓa tsammanin wannan zai kasance maganar mu ta ƙarshe ba.”
Da yake tuna aikin ta a VON, Ndace ya bayyana rawar da ta taka wajen shirya shirye-shirye irin su VONSCOPE, Sixty to Minutes, da Africa Hour.
Ya ƙara da cewa: “Baya ga nasarorin ta na aiki, Hajiya Salami ta kasance mai ƙwarin gwiwa wajen al’amuran ƙungiyoyi, mai tsayin daka wajen kare daidaiton jinsi, kuma malama ga ɗimbin mutane a cikin masana’antar watsa labarai.”
“Shigar ta cikin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Mata ta Ƙasa (NAWOJ), Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), da kuma sake zaɓen ta kwanan nan a matsayin Ma’ajin ƙungiyar IPI sun nuna jajircewar ta ta tsawon rayuwa wajen cigaban aikin jarida da kare haƙƙin ɗan’adam.
“Ta kasance Musulma mai tsantsar addini kuma memba mai aiki tuƙuru a ƙungiyar Al-Habibiyyah Islamic Society, inda Salami ta zama abin misali na rayuwa cike da imani da hidima.
“Taimakon ta wajen ƙarfafa bayar da jini da kuma sadaukarwar ta marar yankewa wajen tallafa wa marasa lafiya sun zama alama ta jinƙai da tausayi nata.
“Tunanin mu da addu’o’in mu suna tare da ɗan ta, Ahmad, wanda take matuƙar ƙauna.
“Muna roƙon Allah (SWT) ya ba iyalan ta ƙarfin jure wannan babban rashi, kuma ya sa Aljannatul Firdaus ce makomar ta.”
“Tarihin Mqdam Salami na tausayi, juriya, da hidima za su ci gaba da kasancewa abin koyi gare mu har abada.
“Allah ya sanya kyawawan tunanin rayuwar ta ta ban mamaki da tasirin da ta bari su kasance masu kwantar da zuciya ga duk waɗanda ke jimamin rashin ta.”