Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya karyata jita-jitar da aka yada a kafafen sada zumunta cewa ya ki amincewa da wanda, Nasir El-Rufai ya kawo ya maye gurbinsa a matsayin minista.
El-Rufai na cikin mutane 48 da shugaban kasa, Bola Tinubu ya aika wa majalisar dattawa, amma har yanzu majalisar ba ta tabbatar da shi ba sabida rahotannin tsaro da aka aike wa majalisar akan shi.
Bayan da aka ki tabbatar da shi, El-Rufa’i ya gana da Tinubu a makon da ya gabata, inda ya shaida masa cewa ba ya sha’awar zama minista amma ya bada sunan tsohon kwamishinansa, Jafaru Sani ya maye gurbinsa.
Sai dai Gwamna Uba Sani ya musanta rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa, shi a ganawarsa da shugaba Tinubu ya ki amincewa da sunan Jafaru sabida shi mai tsantsar biyayya ne ga El-Rufai.