Minista Ya Bar Aiki Saboda Shara Karya

Sabon Ministan Harkokin Wajen Holland, Halbe Zijlstra ya sauka daga mukaminsa bayan sharara karya kan ganawar da ya ce ya yi da shugaban Rasha Bladimir Putin shekaru 12 da suka gabata.

Cikin hawaye ministan ya shaida wa Majalisar Dokokin kasar cewar, ba shi da abin yi da ya wuce ya mika wa sarkin kasar takardar sauka daga mukaminsa.

Gabanin saukarsa, an shirya cewa, yau ranar Laraba ne Ministan zai tafi birnin Moscow domin ganawa da takwaransa Sergei Labrob game da kakkabo jirgin Malaysia a shekarar 2014.

Firaminista Mark Rutte ya bayyana abin da ya faru a matsayin babban kuskuren da ya taba yi a rayuwarsa.

 

Exit mobile version