Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da su riƙa bin ƙa’idojin adalci da sahihanci a cikin rahotannin su da suka shafi Nijeriya.
Idris ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga BBC a ofishin sa a ranar Alhamis.
- Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 5 Da Karbar Wadanda Suka Yi Saranda 44 A Borno
- Al’ummar Arewa: Bango Ne Ya Tsage Kadangare Ya Samu Wurin Shiga
A wata sanarwa da Mataimakin Ministan na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar, an bayyana cewa ministan ya ce yayin da manufofin gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida, gwamnati na sa ran ƙungiyoyin yaɗa labaran duniya su tabbatar da gaskiya da adalci a cikin rahotonnin su.
Ministan ya jaddada muhimmancin daidaito da rashin son kai wajen bayar da rahotanni, kuma ya bayyana cewa yayin da Nijeriya, kamar kowace ƙasa, take fuskantar ƙalubale, yana da matuƙar muhimmanci kafafen yaɗa labarai na duniya su ba da cikakken bayani, maimakon mayar da hankali kan abubuwa marasa kyau.
Ya ce, “Za mu kuma roƙe ku da ku ci gaba da daidaita labaran ku don jin ta bakin mu kan labari. Ba kawai munanan abubuwan da ke fitowa daga Nijeriya ba, akwai abubuwa masu kyau da yawa kuma na tabbata wakilan ku da ke nan sun ga cewa muna da abubuwa masu kyau da muke yi a ƙasar nan kuma akwai cigaba zuwa ga wadata da muke gani.
“Ina so in bayyana maku ƙudirin gwamnatin Nijeriya ga kowace ƙungiya mai tattara labarai. Ƙudurin mu shi ne cewa muna son mu kasance cikin mai da hankali da rashin son zuciya kuma cikin ‘yanci.”
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin Nijeriya ba ta samu wani rahoto da ya shafi cin zarafin ‘yan jarida da ke aiki da kafafen yaɗa labarai na duniya a ƙasar ba.
Ya ce, “Manufar gwamnatin Tinubu ita ce kowace ƙungiya ta labarai tana da ‘yancin gudanar da wannan sana’a kuma ina farin ciki da ba ku kawo mana rahoton wani ma’aikacin ku ba, wanda aka ci zarafin sa ko kuma ya fuskanci matsin lamba daga gwamnatin Nijeriya ba.”
Idris ya yaba wa irin hazaƙar da BBC ta yi wajen mayar da ɗakin watsa labarai na Sashen Hausa daga birnin Landan zuwa Abuja, inda masu kallo da kasuwanni suke, yana mai jaddada cewa wannan gagarumin shiri ya sa aka haɗa ‘yan Nijeriya kusan 200 da ke aiki da BBC a faɗin ƙasar.
Ministan ya bayyana jin daɗin sa da ɗorewar amana da mutunta juna tsakanin BBC da masu saurare a Nijeriya, dangantakar da ke da ƙarfi tun kusan shekaru 60.
Ya ce, “Haƙiƙa al’ummar Nijeriya abokan haɗin gwiwa ne da BBC kuma wannan ƙawancen ya fara shekaru da dama da suka wuce kuma ba a daina wannan sadaukarwar da muka ji a BBC da kuma mutuntawa da amincewar mutanen mu tun shekaru biyar zuwa sittin da suka gabata.”
Ya jinjina wa BBC kan yadda ta fara aikin gina ƙwarewar wasu ‘yan jarida da ke aiki da ƙungiyoyin yaɗa labarai na gwamnati, ya kuma yi kira ga BBC da su yi makamancin hakan ga kafafen yaɗa labarai masu zaman kan su.
A nasa jawabin, Daraktan Labaran Duniya kuma Mataimakin Shugaban BBC, Mista Jonathan Munro, wanda ya zo Nijeriya a karon farko, ya ce ya yi matuƙar farin ciki da shaharar BBC a ƙasar.
Ya ce BBC ta faɗaɗa zuwa kafofin watsa labarai da yawa a Nijeriya kuma yanzu tana yaɗa shirye-shiryen ta a cikin harsunan Pijin da Hausa da Ibo da kuma Yarbanci domin isa ga masu sauraro daban-daban a ƙasar.
Mista Munro, wanda ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai ƙarfin faɗa-a-ji a duniya, ya ce kimanin mutane miliyan 30 ne ke ziyartar sashen labarai na BBC a Nijeriya a duk mako, wanda hakan ya sa Nijeriya ta zama ta uku a duniya wajen tallata BBC bayan Amurka da Indiya.
Mista Munro ya samu rakiyar Shugaban Harsunan Yammacin Afirka, Ehizojie Okharadia; Shugaban Sashen Labarai na Afirka, Juliet Njeri, da Shugaban Sashen Hausa na BBC, Malam Aliyu Tanko.