ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Nemi A Ƙara Ƙulla Danƙon Zumunci A Tsakanin Nijeriya Da Kamfanin BBC

by Sulaiman
1 year ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira da a zurfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da BBC domin samar da al’umma mai masaniya a kan harkokin yau da kullum.

Idris ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai hedikwatar BBC da ke birnin Landan.

ADVERTISEMENT
  • An Bude Baje Kolin Manyan Bayanai Na Kasa Da Kasa A Kasar Sin
  • NCC Ta Tsawaita Haɗa Lambar NIN Da Layukan Waya Zuwa Watan Satumba

Ziyarar dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Nijeriya da kafafen yaɗa labarai daban-daban, na gida da waje.

LABARAI MASU NASABA

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

A ziyarar,  an yi nasarar ganawa da manyan shugabannin BBC, ciki har da Mataimakin Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na BBC kuma Daraktan BBC, Jonathan Munro.

Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen tsara fahimtar jama’a da haɓaka ci gaba.

Ya ce: “Kafofin watsa labarai suna taka rawa mai muhimmanci wajen tsara labaran da suka dace, da samar da fahimtar juna, da samar da cigaba, don haka ya zama wajibi ga kafafen yaɗa labarai da ke isar da saƙo ga duniya su zurfafa fahimtar yanayin zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da al’adun al’ummomin da suke ba da rahoto akai.”

Idris ya kuma bayyana muhimmancin rawar da BBC ke takawa wajen bayar da rahotanni kan tafiyar siyasar Nijeriya, yana mai cewa yana da muhimmanci BBC ta daidaita rahotannin da take yi kan Nijeriya ta hanyar mai da hankali kan cigaban da ƙasar ke samu.

Ya ƙara da cewa, “Nijeriya tana da ɗimbin matasa masu tasowa da ƙaunar da ba a saba gani ba na cin gajiyar damarmaki ko da kuwa ana fuskantar ƙalubale masu tarin yawa, lamarin da ke buƙatar a ba da muhimmanci ga sakamako mai kyau a Nijeriya.”

Ya kuma yi nuni da cewa yaɗa labaran ƙarya babbar matsala ce da ke kawo cikas ga cigaba da kuma lalata amanar da ke tsakanin gwamnati da jama’a.

Idris ya yi kira ga BBC da ta yi aiki tare da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa don magance waɗannan matsalolin.

Ministan ya yaɓa da yadda BBC ke faɗaɗa ayyukan su a Nijeriya ta hanyar samar da ƙarin yarurrukan da suke gabatar da shirye-shirye da su, wato Hausa, Ibo, Yarbanci, da Pijin.

Ya ce hakan ya taimaka wajen yaɗa bayanai da yawa tare da samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da dama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Next Post
Za Mu Tabbatar An Yi Zaben Gwamnoni Lafiya Ba Tare Da Tangarda Ba A Kebbi – ‘Yansanda

‘Yansanda Sun Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Sojoji Suka Yi Wa DPO Wasagu A Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.