Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya shaida a taron da aka gudanar Laraba a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York cewa, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da dukkan bangarorin dake cikin tsarin shirin ci gaban duniya ko GDI, wato shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar shekaru uku da suka gabata a MDD.
Da yake jawabi a taron mai taken “Shirin ci gaban duniya na goyon bayan kasashe masu tasowa — kasar Sin tana aiki”, Wang ya ce, a cikin shekaru uku da suka gabata tun bayan kafuwar GDI, shirin ya sauya daga shawarar kasar Sin zuwa matsayar kasashen duniya, kuma daga manufar hadin gwiwa zuwa aiwatar da ayyukan hadin gwiwa, da ba da gudummawar shawarwarin kasar Sin, da sanya karfin kasar Sin wajen aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD ta shekarar 2030.
Da yake bayyana goyon baya da ayyukan kasashe sama da 100 da kungiyoyin kasa da kasa 20 a shirin na GDI, da kuma gagarumar nasarar da shirin ya samu a fannin tsare-tsare masu inganci, Wang ya ce, babu wata kasa da za a bari baya a cikin tsarin zamanantar da duniya, kuma GDI na ba da fifiko wajen tallafawa ci gaba da farfado da kasashe masu tasowa na duniya. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)