Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a taron manema labarai yau Alhamis cewa, ministan harkokin wajen kasar Birtaniya David Lammy zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 18 zuwa ta 19 ga wata.
Mao ta ce, ziyarar ta zo ne bisa gayyatar da Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi masa. Mao ta kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Birtaniya a matsayin abokan hulda, da riko da gaskiya da hadin gwiwa, da sa kaimi ga samun moriyar juna, da samun nasara tare, da raya ci gaban dadaddiyar dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya.
A wani ci gaban kuma, a martaninta ga rahotanni na cewa, mahukuntan Taiwan ta sanar da fara gudanar da sabon ofishinta a Mumbai na kasar Indiya. Mao ta ce, kasar Sin na adawa da duk wani nau’i na tuntuba da mu’amala a hukumance tsakanin yankin Taiwan da kasashen dake da huldar diflomasiyya da kasar Sin, gami da kafa hukumomin wakilcin juna. Kasar Sin ta yi kakkausar suka ga bangaren Indiya. (Yahaya)