An zabi Sanata Mohammed Monguno daga Borno ta Arewa a matsayin sabon mai tsawatarwar masu rinjaye a Majalisar Dattawa, wanda zai maye gurbin Sanata Ali Ndume.Â
Hakan ne na dauke ne cikin wata wasika da aka aike zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wanda shugabannin jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Ajibola Bashiru suka sanya wa hannu.
- Majalisar Dattawa Ta Tsige Ndume A Matsayin Mai TsawatarwaÂ
- Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Cire Rubutun Ajami A Kudin Nijeriya
Wasikar ta yi korafe-korafe game da sukar da Ndume ya yi a baya-bayan nan game da gwamnati mai ci da jam’iyyar APC.
Shugabannin jam’iyyar APC sun damu game da alaman Ndume, musamman lokacin da ya alakanta gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ci hanci da rashawa.
Sun ce wadannan kalamai sun zubar da kima da martabar jam’iyyar.
Kwamitin gudanarwa na jami’yyar na kasa, ya shawarci Ndume kan fice daga jami’yyar.
Don magance wadannan matsaloli, APC ta aike da sunan Monguno a matsayin sabon mai tsawatarwar Majalisar Dattawa.
Sun bukaci kwamitin majalisar dattawa da ya tabbatar da cewa mambobin kwamintinsa suna yin magana cikin gaskiya a bainar jama’a don tabbatar da hadin kai da kuma yi wa ‘yan Nijeriya hidima.