Hukumar lafiya ta duniya ta ja hankali inda tace mutane kusan milyan 500 na iya kamuwa da cututtuka masu hadari,irin masu alaka da zuciya a duniya,kiba,cutar sikari,da sauran cututtuka wadanda kamuwa dasu nada nasaba da rashin motsa jiki.Wannan kuma nan da shekara ta 2020 zuwa 2030.
WHO awani rahoton shekarar 2022 data fitar na duniya dangane da motsa jiki wanda aka wallafa ranar Laraba ta makon daya gabata ta bayyana cewa mutane milyan 500 na iya kamuwa da muggan cututtuka tsakanin shekarar 2020 da 2023.Wannan kuma ya danganta ne idan har su gwamnatoci kasashen duniya sun ki daukar matakin da zai inganta amfanin motsa jiki ga al’umma.
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
- Ya Zama Wajibi Al’umma Su Fito Don Zabar Shugabanni Masu Adalci – Wakili
Shi rahoton dangane da al’amarin daya shafi motsa jikina shekarar 2022 yayi nuni ne akan bukatar da ake da ita ta yin amfani da shawarwarin da aka bada na bukatar kara yawan motsa jiki,wannan ba a kaiyade ga shekarun da ake bukatar motsa jikin ba kowa yana iya motsa jikinsa.
Bayanan da aka tattaradaga kasashe 194 ya nuna irin cigaban da aka samu gaba daya, babu wani cigaban da za a iya cewa an samu, saboda abin yana tafiyar Hawainiya ne don haka ne su kasashen ua dace su fara amfani da su shawarwarin tsare- tsaren da zasu taimaka wajen bunkasa bugawar Zuciya, daukar matakan da za su taimakawa wajen hana kamuwa da Cututtuka, da kuma rage ayyukan kula da lafiyar al’umma kan cibiyoyin kula da lafiyar.
A taimakawa kasashe su kara al’amarin daya shafi motsa jiki, kamar yadda tsarin dokar motsa jiki na duniya ya bayyana tsakanin shekarar 2018-2030, ya fitar da tsare- tsare da shawarwari 20.
Wadannan shawarwarin sun hada da hanyoyi masu kyau tare da karfafawa mutane da basu kwarin gwiwa,kan hawan keke,da kuma tafiya,ga kuma samar da karin tsare tsare,ga kuma bada dama, ta al’amarin motsa jiki,kamar kulawa da kananan yara, kananan asbitoci, da kuma wuraren aiki.
“Ana rasa abubuwan da duniya ta amince dasu na hanyoyi zuwa wuraren shakatawa, hanyar amfani da keken hawa, da kuma hanyar tafiya ta kasa duk kuwa da yake akwai irin hakan a wasu kasashe,” cewar Fiona Bull, da yake shi ne shugaban sashen motsa jiki kamar yadda yace.
Hakanan ma, ba wani bayani ko rahoto kan wani cigaban da aka samu na samar da abubuwan more rayuwa da zasu taimaka wajen karuwar motsa jiki.
“Abin zai iya kasancewa ba wani abin azo a gani na cigaba domin ba abinda ke nuna lalle babu wasu tsare- tsare ko zuba jari.
“Abinda ya dace ayi shi ne za ayi da yake akwai yadda za’a cimma burin motsa jiki kamar yadda ya dace,”Ms Bull tace haka a wani bayani said in a statement.
Rahoton yayi kira da kasashe dasu dauki al’amari motsa jiki a matsayin wata hanyace ta inganta lafiya da kuma maganin kamuwa da muggan cututtuka, ta yin amfani da tsarin motsa jiki a wasu tsare- tsaren da suka dace domin samar da abubuwan da za yi amfani dasu wajen horarwa.
“Yana dakyau ga kula da lafiyar al’umma da ala’amarin daya shafi tattalin arziki wajen inganta karin motsa jiki, ga kowa da kowa a cewar,” Ruediger Krech”.
Ya dace mu harzarta shigar da manufofin da suka dace kan motsa jiki ga kowa da kowa da kuma tabbatar da mutane sun samu damar da za su motsa jikinsu ba tare da fuskantar matsala ba.
Wannan rahoton yayi kira ga dukkan kasashe da masu ruwa da tsaki su dauki duk matakan da suka dace na cimma muradan a kalla kashi 15, sai kuma kawo karshen irin yanayin da za a iya shiga sanadiyar rashin motsa jiki nan da shekara ta 2030 shekara ta 2030.