Mourinho Ya Tauye Wa Mkhitaryan Hakkinsa A United, In Ji Rooney

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Wayne Rooney ya bayyana cewa an tauyewa tsohon dan wasan kungiyar, Henrikh Mkhitaryan hakkinsa a Manchester United.

Rooney yace, tun farkon zuwansa kungiyar yaga alamun cewa dan wasan kwararre ne sosai kuma yanada gudunmawar da zai bawa kungiyar yadda yakamata sai dai hakan bata samu ba.

Yaci gaba da cewa dan wasan yana bukatar buga wasanni sosai a akungiyar kafin duniya ta gane kwarewarsa sai dai kungiyar bata bashi wannan damar ba kuma a karshe suka rabu dashi.

Sai dai yace kungiyar kamar Manchester United sai dan wasa ya dage sosai kafin yasamu damar data cancanta kuma kowanne dan wasa ma zai iya samun kansa a irin wannan yanayi.

Rooney da Mkhitaryan dai sun buga gasar wasa guda daya a kungiyar kafin daga baya Ronney yakoma tsohuwar kungiyarsa ta Eberton a cikin watan Agustan shekarar data gabata.

A satin daya gabata ne Arsenal ta lallasa Eberton din Rooney daci 5-1 kuma har da Mkhitaryan acikin yan wasan tawagar Arsenal bayan yakoma Arsenal yayinda shi kuma Aledis Sanches yakoma Manchester United a cikin watan Janairun daya gabata.

Exit mobile version