Mu Na Da Ayar Tambaya Kan INEC, Cewar Daraktan Kamfen Din Atiku

ALHAJI YAHAYA BAGOBIRI shi ne daraktan yakin neman zaben a Kano na dan takarar shugabancin Najeriya a babbar jam’iyyar hamayya ta kasa, PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar. A tattaunawarsa da wakilin LEDARSHIP A YAU LAHADI, HARUNA AKARADA, ya bayyana yadda su ke da karfin gwiwa da aminci a kan dan takarar da su ke mara wa baya, kwarewarsa, gogewarsa gami da tsammanin da su ke ma sa na lashe zabe a shekara ta 2019.

Da farko za mu so ka gaya mana ko akwai wata cancanta da Atiku abubakar ya ke da ita ta zama shugaban kasar Najeriya kuma wane kokari za ku yi wajen ganain ya sami nasara?

Mu na yi wa Allah godiya, mu na sake yi ma sa godiya saboda kasancewar Mai girma Wazirin Adamawa ya sami nasarar tsayawa takara a taron da a ka yi a birnin Fatakwal a farkon watan da ya gabata. Allah muna gode maka. Bayan wannan kuma ka yi min tambaya, cewa wace irin kokawa za mu shiga wajen ganin wazirin Adamwa ya sami nasara. Ina tsammanin dai haka ne ko? To cikin yardar Allah kamar yadda aka sani, Wazirin Adamawa mutum ne jajirtacce, mutum ne mai kwazo, mutum ne mai kokari a duk fannin da ya sami kansa. Ya taba samun kansa a matsayin jami’in hana fasa kwauri (Nigerian custom serbice), wanda ya yi iyakcin iyawarsa wajen ganin ya yi aiki tukuru don bunkasa tattalin arzikin kasar nan. Bayan gama aikin custom ya zama babban dan kasuwa wanda kusan a Afirka da duniya yana cikin manyan ‘yan kasuwa. Bayan wanann, ya sami kansa cikin harkokin siyasa tun daga lokacin mai girma Shehu Musa ‘Yar Aduwa suka hadu a juanansu suka kago PF People Front of Nigeria, ya zamanto shi ne kamar mai tallafawa Shehu Musa ’Yar Aduwa Allah ya ji kansa. Bayan rasuwar Shehu Musa ’Yar Aduwa sun yi jam’iyyar nan wadda ake cewa PDM. Daga nan aka taho aka zo jam’iyyar SDP, ya ma yi takara ta shugabancin kasar nan a 1991, wanda aka yi babban taro a Plateau. Duk da ba a sami nasara ba amma anci gaba da gwagwarmaya. Yanayi ya nuna cewa shi dan siyasa ne, kuma ya zma zababben gwamna a Adamawa a 1999. Kafin a rantsar da shi kuma aka tabbar da shi a matsayin mataimakin shugaban Taraiyar Nigeria. Mutum ne mai kokari kwarai da gaske a duk halin da ya sami kansa kwarai.

Kuma yanzu ga shi Allah cikin ikonsa, bayan gwagwarmaya da ya yi ya tsaya takarkaru daban daban har sau uku. Wannan ita ce gagarumar nasara da Allah ya ba shi a Port Harcourt Conbention. Kuma yanzu zai kara da jam’iyyar APC. Ita wannan jam’iyya ta APC, kowa ya san al’ummar Najeriya sun gaji da ita. Ta gaza ta fanni daban daban na tattalin arziki, bangaren rashin aikin yi, bangaren harkar lafiya da ilimi. Abin da ya shafi rayuwa ta dan Adam yau da kullun. Hauhawar farashin kaya, tashin farashin man fetur da dai sauransu. Wanda shi a matsayinsa na kwararre wanda ya kware a fannukan can guda uku da na lissafa maka: aiki kasuwa da siyasa, to ina ganin cikin yardar Allah za a sami farfadowar tattalin arzikin kasa talaka ya dawo cikin haiyacinsa.

 

Ganin yadda Najeriya ta a yau, wacce hanya Atiku Abubakar zai bi wajen ganin ya gyara al’amura a Najeriya idan ya lashe zaben 2019?

To ai an ce masanin hanya shi ake mika wa linzami. kamar yadda na fada maka shi Alh. Atiku Abubakar ya kware a fannin tattalin arzikin kasa, ya kware a fannin aiyuka, ya kware a fannin siyasa. To da wahala mutum ya sami wannan gogaiyar ta abubuwa uku, kuma ya zamo ba shi da tausayi ko imani ga talakawa. Shi ya sa ma in ka duba, tun da aka kammala taron can na birnin fatakwal aka sanar da cewa Atiku Abubakar ya sami nasara, mutane suke ta cewa ‘Akori yunwa ya zo’. ‘Mai maganin matsin nan ya zo.’ Don haka, duk inda ka kewaya a taraiyar Najeria za ka ji ana cewa Atkiu za a yi a 2019. Wannan ya nuna mutane suna da kyakkyawan fata a kansa.

 

Ku na ganin Atiku zai iya kayar da shugaba mai ci yanzu, Janar Muhammadu Buhari?

Kayarwa kamar yaya? Kokawa ta mutum da mutum? Idan kokawa ce ta mutum da mutum ka san Atiku Abubakar hannu daya zai sa ya ture shi. Cin zabe kuma na Allah ne, amma dai mun san Allah shi ke da gobe. Yanzu mu dauki yankunan nan guda shida na tarihi da a ke da su (6 geographical zones), ka dauki Kudu Maso Gabas yankin Inyamurai da ma su ba su san wata jam’iyya ba ma in banda PDP. Ka dauki Kudu Maso Kudu da ma nan PDP ce baki-daya. Jihohin yamma, jihohin Yarabawa da ma wake-da-shinkafa ne gurin. To, yanzu, duka abu daya za a yi bakidaya cikin yardar Allah. Ka ga yankin kudanci kenan a dunkule, kuma in dai zabe za a buga ko ba ni da rai sai ka zo ka ce abin da na fada haka ya ke zai faru.

 

To, amma duk jihohin can da ka lissafa ai ba su kai ’yan Arewacin Najeriya ba, ko?

To, mu dawo Arewan. Tun da Nan ka fi wayo ni ma nan na fi wayo. Arewa ta Tsakiya shi ne North Central, wadda ta kunshi Kwara Kogi, Nasarawa, Plateau, Benue da Taraba, haka ne? To wannan yankin cikin yardar Allah PDP ce za ta lashe shi, in dai an doka zabe. Wannan yanki ba ni da shakku Waziri zai lashe shi. Ka ga yanki hudu kenan. Mu tafi Arewa masu Gabas, shi nan gidansa ne, yankinsa ne. Mu na ganin wannan yankin cikin yardar Allah gida za su yi. Yankin Maiduguri, Yobe, Bauci Adamwa da Gombe. Bari in zo ta shidan. Ita ce Arewa maso Yamma inda ka ke, na ke, Buhari ya ke. Nan ne mu ka fi yawan al’umma, nan ne muka fi yawan kananan hukumomi, nan ne mu ka fi yawan mazabu a tarayyar Najeriya, nan ne mu ka fi yawan marasa aikin yi, nan ne mu ka fi yawan masu zaman banza. Kuma nan mu ka fi yawan masu shaye-shaye, nan ne mu ka fi yawan rashin sana’a. Abubuwa da dama wannan yanakin na Arewa maso Yamma ya ke fama da su. Kuma Kano ita ce babbar gidan Buhari a siyasa. Ina tabbatar ma ka a halin da a ke ciki mutanen Kano ba wawaye ba ne, ba mahaukata ba ne, su na da ilimi na kowane fanni. Kuma sun san abin da ke damun su.

A yanzu da na ke ma ka magana, ba wata kauna ko soyayya da Buhari ya ke wa mutumin Kano. Dalili na a nan shi ne, abubuwa daban-daban sun faru a nan Kano. Mun rasa manya-manayan malamai a Kano, Buhari bai taba takowa ya ce Allah ya ba da hakuri ba. Masifu da bala’o’i iri-iri da ibtil’i ya samu a jihar Kano na gobara da rasa dukiya mai tar in yawa na bilyoyin nairori, Buhari bai taba zuwa ya ce da mutanen Kano Allah ya kiyaye ko Allah ya mai da alheri ba. Zancen da na ke gaya maka, ka ajiye siyasa, ka je ka yi hira da mutanen kasuwar Sabon Gari, ka yi hira da mutanen Kantin Kwari, ka yi hira da mutanen Kasuwar Kurmi, duk ka ji shin abin nan da na fada haka ne ko ba haka ba ne. Sabo da haka, hatta jihar Katsinan ma, da Zamfara da Sokoto, Kebbi, Kaduna da Jigawa, ina tabbatar maka cewa Mai girma Wazirin Adamawa duka daya zai lashe zabe cikin yardar Allah. Wannna shi ne atakaice.

 

Daga karshe, ya ya ku ke kallon kamun ludayin ita hukumar zabe. Kun yaba da yadda ta ke shirye-shiryenta ko ku na ganain akwai inda za ta gyara?

Yadda mu ke kallon ta shi ne ta na kokari, duk da ba za mu ce dari-bisa-dari ba, domin ka san idan mutane su na gonarka su na yi ma ka aiki ba ka rasa masu dan yin tsumbure ba. To har yanzu dai muna da ’yar ayar tambaya kadan a kan hukumar zabe tattare da la’akari da zabuka na cike gurbi da aka yi a wasu jihohi. Mu na ganin an yi amfani da gwamnati, an yi amfani da karfin mulki an take dokoki da tsarin mulki Najeriya. Tunda akwai inda ma mu ka ci zaben, amma aka ki baiyanawa. A ka zo a ka bar wasu ‘yan guarare a karshe aka zo aka bibbige aka karkashe mutanenmu aka sanar da sakamkon da ake so. Duk ka ga wannan yana sanyaya guiwa. Amma dai muna ganin ita hukumara zaben nan ta ‘yan kasa ce, kuma muna jawo hankalinta cewa ita ce za ta yi jagora a kai ga nasara kasar nan ta dore ta zauna lafiya. Muna jawo hankalinsu da su yi iyakacin iyawarsu su ga yadda Najeriya za ta dore a matsayin kasa dunkulalliya ba za a sami matsala ta hanayoyin zabe ba. Ba don komai ba, saboda an yi zabukan 2015, ba za mu ce babu ind aka sami kurakurai ba, to amma dai ‘yan kasa sun ji dadin abinda abubuwan ya faru kuma kasa ta cigaba da zama lafiya. To fatanmu a wannan karon ma shi shugaban hukumar zabe na yanzu Farfesa Mahmud Yakubu ya kwatanta adalci yadda mutanen za su karba su gamsu da shi.

Exit mobile version